Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fi kowace gwamnatin Soja da Nijeriya ta taɓa yin muni wajen tafiyar da mulki.
El-Rufai ya bayyana haka ne a lokacin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai masa ziyara ta musamman a Kaduna a ƙarshen mako, bayan harin da aka kai wajen taron ƙaddamar da jam’iyyar ADC a jihar.
- APC Na Ƙoƙarin Tarwatsa Mu Ne Saboda Kar Mu Ƙwaci Mulki A 2027 – ADC
- INEC Ta Amince Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC
A cewar El-Rufai, gwamnatin Tinubu ta karkata zuwa mulkin danniya da kama-karya, inda ya kwatanta shi da Shugaban Kamaru, Paul Biya, wanda yake riƙe da mulki tun 1982. Ya zargi gwamnatin da ƙoƙarin mayar da iko hannun gwamnatin tarayya maimakon zurfafa tsarin tarayya. “Idan ba mu haɗu mun ƙori wannan gwamnatin a 2027 ba, Tinubu zai zama mana tamkar Paul Biya,” in ji shi.
Ya jinjina wa Atiku a matsayin jagoran adawa, yana mai cewa jama’a suna sa ran ƙwarewarsa a gwagwarmayar dimokuraɗiyya.
Ana sa jawabin Atiku Abubakar, ya yi kira ga shugabannin adawa su tsaya tsayin daka tare da haɗa kai domin tabbatar da kawar da Tinubu ta hanyar zaɓe a shekarar 2027.














