Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin karatun duk wanda ya haddace Alƙur’ani kuma yake son ci gaba da ilimi a fannonin zamani kamar likitanci, ungozoma da sauran sana’o’in zamani.
Ya bayyana haka ne a babban taron da aka gudanar domin gyara tsarin karatun Almajiri da Islamiyya a jihar, inda malamai, shugabannin al’umma, ƙungiyoyi da hukumomi suka halarta.
- Yadda Aka Bai Wa Ousmane Dembélé Kyautar Ballon d’Or Ta 2025
- Sin Tana Maraba Da Kwararru Daga Bangarori Daban Daban Na Kasa Da Kasa Su Zo Kasar
Gwamnan ya ce gwamnati za ta kafa sabbin makarantu guda uku da za su haɗa mahaddata Alƙur’ani da ilimin zamani irin su Turanci, Lissafi da koyon sana’o’in hannu ga yara maza da mata.
Makarantar farko za ta kammalu a Katsina kafin ƙarshen nan.
Ya kuma jaddada cewa malamai za su taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar wannan shirin, tare da kira ga iyaye da al’umma da su bayar da goyon baya domin gwamnati kaɗai ba za ta iya magance matsalar almajiranci ba.
Masana da shugabanni da suka halarci taron, ciki har da Farfesa Isah Ali Pantami, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da sauran fitattun malamai, sun yaba da wannan ƙudiri na gwamnatin Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa sama da yara 300,000 ne ba sa zuwa makaranta a Katsina, ciki har da dubban almajirai da ‘yan mata.
Wannan ne ya sa gwamnati ta ɗauki wannan mataki domin inganta ilimi da kuma bai wa matasa damar samun kyakkyawar makoma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp