Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce a nan gaba kamata ya yi Sin da Amurka su lalubo hanyar da ta dace ta tafiya tare a sabon zamani. Li, ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin zantawarsa da rukunonin kawancen Sin dake Amurka, ciki har da wakilai daga kungiyar ‘yan kasuwa ta Amurka da Sin, da kwamitin kasa na inganta alakar Amurka da Sin, da cibiyar bunkasa cinikayya ta Amurka, da majalisar bunkasa alaka da kasashen ketare, da malamai da jagororin ‘yan kasuwa.
An gudanar da zaman ne a gefen babban taron mahawara na MDD karo na 80 dake gudana a birnin New York na Amurka, inda Li ya ce a matsayinsu na manyan kasashen duniya biyu, ya dace Sin da Amurka su martaba juna, su yi cudanya cikin lumana, da cimma nasarar hadin gwiwar moriyar juna, da samun wadatar bai daya.
Li, ya ce Sin na da karfin gwiwa, da ikon wanzar da ci gaban tattalin arziki mai karko da daidaito, da samar da karin damammaki ga kamfanoni dake dukkanin sassan duniya ciki har da kamfanonin Amurka. Ya kuma bayyana fatan ganin dukkanin al’ummun Amurka sun aiwatar da matakai na inganta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, da fadada hadin gwiwa na zahiri a mabanbantan sassa, tare da bayar da babbar gudummawar ingiza ci gaban kasashen biyu da kyautata kawancensu.
Wakilai daga bangaren Amurka da suka halarci zaman sun amince da kyawawan nasarorin da Sin ta cimma a fannin raya tattalin arziki, da kirkire-kirkiren fasahohi, da raya zamantakewar bil’adama da sauran fannoni a shekarun baya bayan nan.
Rukunin ‘yan kasuwar Amurka mahalarta zaman sun bayyana kwarin gwiwarsu game da bunkasar tattalin arzikin Sin, tare da bayyana aniyarsu ta ci gaba da fadada zuba jari a Sin, ta yadda za su taka rawar gani a fannin cike gibin dake akwai, tare da ingiza hadin gwiwar kasashen da kara kyautata fahimtar juna. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp