Tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka bisa jagorancin Adam Smith ta kammala ziyara a kasar Sin a jiya Alhamis 25 ga wannan wata, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun maida hankali sosai kan batun.
Kafin ziyarar tawagar, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun zanta ta wayar tarho, da yin musayar ra’ayoyi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da batutuwan da suke sa lura tare, kana sun tsara taswira kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kama a mataki na gaba. Bisa wannan yanayi, ziyarar tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka ta shaida muhimmiyar rawar manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara, da ci gaba da karfafa mu’amalar dake tsakanin manyan jami’an kasashen biyu, wannan ne mataki mai muhimmanci wajen kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.
Farfesa na kwalejin nazarin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa na jami’ar Renmin ta kasar Sin Diao Daming ya yi nuni da cewa, ziyarar tawagar membobin majalisar wakilai ta Amurka a kasar Sin a wannan karo ta taimaka wa membobin majalisar su kara sanin hakikanin halin kasar Sin, da kara fahimtar kasar Sin, ta haka za su nuna ra’ayi bisa tushe yayin da suke tattauna batutuwan dake shafar kasar Sin.
Kamar yadda kasar Sin ta jaddada a yayin tattaunawar, ana fatan majalisar wakilan Amurka za ta maida hankali ga kasar Sin da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata, da sa kaimi ga yin mu’amala da hadin gwiwa a tsakaninsu, don taka muhimmiyar rawa wajen sada zumunta da samun bunkasa tare a tsakanin kasashen biyu. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp