Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a Lagos a jiya Juma’a domin ziyarar aiki yayin da ƙasar ke shirin bikin cikar shekaru 65 da samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka.
A cewar kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, Tinubu ya tafi Legas ne bayan ya halarci naɗin sabon Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, a garin Ibadan, jihar Oyo.
- Sarkin Musulmi Ya Taya Ladoja Murnar Zama Sabon Sarkin Ƙasar Ibadan
- Yadda Aka Gudanar Da Taron Tuna Shekara 20 Da Rasuwar Dr Bala Usman
Yayin da yake a Lagos, shugaban ƙasa zai gana da manyan ƴan kasuwa da jiga-jigai a ɓangaren gwamnati domin tattaunawa kan ci gaban tattalin arzikin ƙasa. Haka kuma, a ranar Talata, 30 ga Satumba, zai ziyarci jihar Imo inda zai ƙaddamar da wasu muhimman aiyukan raya ƙasa na Gwamna Hope Uzodimma.
A wani ɓangare na bikin zagayowar ranar ƴancin kai, Tinubu zai kuma ƙaddamar da sabuwar cibiyar al’adu da fasaha ta ƙasa, wadda aka sake fasalta wa daga tsohuwar National Theatre zuwa Wole Soyinka Centre for Culture and the Creative Arts.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp