A wannan sabuwar kakar da aka fara, babu gasar da aka ci kasuwar manyan ‘yan wasan gaba a nahiyar turai kamar kasar Ingila domin a Ingila ne idan ka cire Manchester City kusan duk manyan kungiyoyin gasar sun sayi dan wasan gaba.
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta dauki Biktor Gyokeres daga Sporting Lisbon sai Manchester United wadda ta dauki Benjamis Sesko, ya yin da Newcastle United ta dauki ‘yan wasan gaba guda biyu da suka hada da Nick Woltemade da Yoanne Wissa.
Mai kare kambu sannan wadda take jan ragamar gasar a wannan lokaci, Liberpool, ta dauki manyan ‘yan wasan gaba guda biyu da suka hada da Hugo Ekitike da Aledander Isak. Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ‘yan wasan gaba guda biyu ta dauka, inda ta fara daukar Liam Delap daga Ipswich Town da Joao Pedro, dan Brazil, daga kungiyar Brighton Albion.
Amma duk da haka matashin dan wasa Erling Haaland ya ci kwallaye 13 a kungiyar Manchester City da kasarsa ta Norway daga fara kakar wasa ta bana, har da wadda ya zura a ragar Arsenal ranar Lahadi a Premier League.
Kenan wasanni takwas jimilla ya buga kawo yanzu, masu sharhi suna ganin hakan na nufin zai iya lashe takalmin zinare a fagen cin kwallaye a nahiyar Turai da Premier League idan har aka ci gaba da tafiya a haka.
Haaland ya fara da zura kwallo biyu a raga a wasan da Manchester City ta caskara kungiyar kwallon kafa ta Wolberhampton 4-0 a gasar Premier League ranar 16 ga watan Agusta. Ya kuma ci kwallayen a minti na 34 da kuma a 61 a karawar da aka yi a filin wasa na Molineud a wasan makon farko a babbar gasar Ingila.
Sai dai dan wasan tawagar ta Norway bai ci kwallo ba a mako na biyu a wasan da Tottenham ta doke City 2-0 a Etihad, sai dai daga lokacin ya ci kwallaye a dukkan wasannin da ya buga na gaba. Ranar 31 ga watan Agusta, Manchester City ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Brighton a wasan mako na uku a Premier League, Haaland ne ya fara cin kwallo tun kafin hutun rabin lokaci.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Brighton ta farke ta kuma kara ta biyu da ta kai ta hada maki ukun da take bukata.
Norway ta buga wasan sada zumunta da Finland ranar 4 ga watan Satumba, inda Norway ta yi nasara 1-0, kuma Haaland ne ya ci kwallon a bugun fenariti a minti na 17 da fara wasa. Daga nan Haaland ya zura biyar a ragar Moldoba lokacin da Norway ta sharara 11-1 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya, inda mai tsaron raga, Cristian Abram ya ce Haaland ya je ya bashi hakuri kan yawan kwallaye da Norway ta zura musu.
Da ya koma Ingila, bayan buga wasannin neman shiga gasar kofin duniya, Haaland ya zura kwallo biyu a ragar Manchester United a wasan hamayya a Premier League mako na hudu ranar 14 ga watan Satumba. Daga nan Manchester City ta fara buga Champions League wasan farko a cikin rukuni da doke Napoli 2-0 ranar 18 ga watan Satumba, inda Haaland ne ya fara cin kwallo da suka koma zagaye na biyu a filin wasa na Etihad.
Ranar Lahadi Haaland ya fara cin Arsenal kwallo a Premier League wasan mako na biyar, kuma na biyar da ya ci Arsenal a karawa ta bakwai, sannan kwallo ta 20 daga wasa 21 da ya ziyarci duk wata kungiyar kwallon kafa da take birnin Landan.
Kenan Haaland ya ci kwallo shida a Premier League, sannan bakwai a Manchester City har da wadda ya zura a ragar Napoli a Champions League, jimilla ya ci 13 a karawa takwas a kungiya da kasarsa. Wannan kakar Haaland bai fara da kokari ba duk da cin kwallo shida a wasa biyar a Premier League tun bayan da ya koma Manchester City a kakar wasa ta 2022 zuwa 2023.
A kakarsa ta farko ya zura kwallo tara a raga a wasa biyar da fara kakar gasar firimiya ta Ingila, sai kuma ya ci bakwai a wasa biyar da fara kakar wasa ta 2023 zuwa 2024. Amma a bara 10 ya zura a raga da fara wasan Premier League biyar har da uku rigis da ya ci Ipswich Town da kuma West Ham United.
A kakar nan ya zura kwallo biyu a raga a wasa shi ne a Wolberhampton a Molineud a Premier League da kuma Manchester United a wasan hamayya a filin wasa na Etihad da ke birnin Manchester. Kwallo biyar da Haaland ya sharara a ragar Moldoba ya yi kan-kan-kan da tarihin da ya kafa a baya a Manchester City a fafatawa da RB Leipzig a 2022 zuwa 2023 Champions League da wasa da Luton a FA Cup a 2023 zuwa 2024.
Karo 26 yana cin kwallo uku rigis a raga a tarihi, kuma na biyar a tawagar Norway. Ya ci kwallo uku rigis a Manchester City da karo uku yana zura uku rigis a raga a Norway tun daga lokacin da ya koma buga wasa a Etihad. Ranar 10 ga watan Mayun 2022, Manchester City ta sanar da sayen Erling Haaland daga Borussia Dortmund.
Kofunan Da Haaland Ya Lashe
Red Bull Salzburg
Austrian Bundesliga: 2018–19, Austrian Cup: 2018–19, Borussia Dortmund
DFB-Pokal: 2020–21
Manchester City
Premier League: 2022–23, 2023–24. FA Cup: 2022–23, FA Community Shield: 2024
UEFA Champions League: 2022–23, UEFA Super Cup: 2023.
Norway U17
Syrenka Cup: 2016,
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp