Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi zargin cewa, cikin watanni shida, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya samu karin kaso daga gwamnatin tarayya fiye da yadda ya samu a cikin shekaru 8 da ya yi yana gwamna.
Batun rabon kuɗaɗen wata-wata ga Jihohin dai ya zama abun muhawara a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
- Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa?
- Gwamna Yusuf Ya Aike Da Sunayen Kwamishinoni Zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano
“A yau zan iya bugun ƙirjina kuma kowanne daga cikin gwamnonin nan zai iya tabbatar da cewa, rabon da ake bai wa jihohin ya ninka sau uku, kuma akwai l isassun kuɗaɗe daga ƙananan hukumomi.” in ji Ganduje
Da yake jawabi bayan wani taron masu ruwa da tsaki a Kano, Ganduje ya bayyana cewa, ya nuna shakku kan nasarorin da magajin nasa ya samu, inda ya ce gwamnatin Yusuf na kashe kuɗi ba tare da wani lissafi ba.
Tsohon gwamnan, ya ƙara da cewa, “lokacin da na karɓi mulki, ban taɓa ɓata lokaci ba wajen binciken magabatana, gwamnati tana da yawa, sai dai ka gama ka mika wa wani, amma Abba Yusuf ya fara gwamnatinsa da bincike.
“Ku gaya mani, me suka bankaɗo? Sun samu kuɗi a cikin watanni shida fiye da yadda gwamnatina ta samu a cikin shekaru takwas. To amma, wacce nasara suka samu?”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp