Jami’an tsaro a Jihar Kogi sun ceto mutane takwas daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su har 12 a hanyar Okene–Auchi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansanda ta jihar, William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin a Lokoja ranar Asabar. Ya bayyana cewa fasinjojin suna tafiya ne a cikin motar haya ta Big Joe mai lambar Edo FUG 13 XY daga Abuja zuwa Benin, da Jihar Edo, kafin ƴan bindiga su tare su a hanya.
- Gwamnatin Kogi Ta Yi Haɗin Gwuiwa Don Fara Fitar Da Amfanin Gona
- Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina: Nasara Ko Matsala?
Aya ya ce rahoton sace Fasinjoji yana shigowa, DPO na Okene, Nasir Muhammad, tare da haɗin gwuiwar Sojoji da ƙungiyar sa-kai, suka ƙaddamar da sintiri wanda ya kai ga kuɓutar da mutane takwas ciki har da direban motar.
Ya ƙara da cewa ana cigaba da ƙoƙarin ceto sauran mutane huɗun da ke hannun masu garkuwa da su, tare da tabbatar da cewa za a kamo waɗanda suka aikata wannan ta’asa domin fuskantar hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp