Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta rufe manyan shagunan ƴan China guda biyu da ke unguwar Jabi a Abuja, tare da kulle shagunan kayan shafe-shafe guda takwas a kasuwar Wuse saboda karya ƙa’idojin sayarwa, da rarrabawa da kuma rubuta sunayen kayayyaki.
A cikin sanarwar da mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na hukumar, Adegboyega Osiyemi, ya fitar a ranar Juma’a, an ce wannan mataki ya biyo bayan umarnin daraktar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, inda tawagar NAFDAC ta kwace kayayyakin da ba su dace ba da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 170.
- Shettima Ya Dawo Abuja Bayan Ziyarar UNGA Da Jamus
- NAPTIP Ta Kama Mutum 5 Da Ake Zargi Da Safarar Mutane A Filin Jirgin Saman Abuja, Ta Ceto Mutane 24
Hukumar ta bayyana cewa an rufe shagunan da ke Mike Akhigbe Way da Ebitu Ukiwe Street bayan rahotanni daga masu amfani da kayayyaki da kuma bincike sun tabbatar da cewa shagunan na sayar da abinci da aka rubuta sunayensu da Sinanci kawai, ba tare da fassarar Turanci ba, lamarin da ya saɓawa tsarin Nijeriya. Kuma jami’an NAFDAC sun gano cewa ɗaya daga cikin shagunan yana aiki da cikakken kayan da ba a yi musu rajista ba.
Haka nan, a kasuwar Wuse an rufe shagunan kayan shafe-shafe guda takwas da ake zargi da sayar da kayayyaki da aka haramta, waɗanda wa’adin su ya ƙare, da kuma waɗanda ba su da rajista. Bincike ya gano cewa wasu ƴan kasuwa suna shiga irin ta likitocin fata da masu bayar da magani, suna rubuta kayayyaki masu haɗari ga mutane da nufin sanya fata fari, da gyaran jiki ko ƙara kuzarin jima’i.
Daga cikin kayan da aka kwace akwai magungunan sanya fata fari, da ƙwayoyin ƙara kuzari, da wasu magungunan gargajiya da kayan shafe-shafe da ake danganta su da haɗarin cutar da ƙoda, da fita daga hayyaci da ciwon daji na fata.
Farfesa Adeyeye ta jaddada ƙudirin NAFDAC na kare lafiyar ƴan Nijeriya, tare da shawartar al’umma da su rika amfani da kayayyaki da aka tabbatar da rajistarsu a hukumar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp