Sabaya na daya daga cikin abubuwan da ke inganta lafiyar mace, musamman bayan haihuwa.
Ga wasu daga cikin fa’idodinsa:
- Taimakawa wajen dawo da halittar mace, yana hana jikin mace faduwa ko sauyawa bayan haihuwa, kuma yana tabbatar da cewa ba za ta zube ba.
- Jikinta zai yi laushi da santsi. Sabaya na sa fata ta yi taushi da santsi kamar kwalabiya.
- Kare mace daga ramewa bayan haihuwa. Yana cike gibin da mace ke samu bayan haihuwa, yana hana ta ramewa fiye da kima.
- Yawan ruwan mama da ingancinsa. Sabaya na kara yawan ruwan mama, yana kuma hana shi lalacewa.
Kiwon lafiya ga jariri da magidanci.
Jaririn da aka haifa zai samu kariya daga cututtuka, kuma magidanci idan ya sha yana kara lafiya da kuzari, har ma wajen kusantar iyalinsa.
Abubuwan da ake bukata wajen hada sabaya
Alkama 1 mudu, danyar Shinkafa mudu 1, Waken Suya mudu 1, Ridi daya da rabin mudu, Hulba daya da rabin mudu, Gyada mai bargo/Kamfala, Madara, Zuma.
Yadda ake hadawa:
A soya ridin har sai ya yi kantu.
A soya gyada har sai ta yi irin ta kuli-kuli.
A jika shinkafa da alkama na tsawon awa 5, sannan a shanyasu su bushe.
A hade ridi, gyada, alkama, hulba da
shinkafa sannan a nika su tare har su zama gari.
Ana iya fara ba mace tun tana da ciki har zuwa bayan haihuwa don lafiyarta da ta jaririnta. Yana tabbatar da cewa mamanta zai kasance da kyau, ko da tana shayarwa ko a’a.
Yadda ake sha:
A dama shi kamar yadda ake kunu, amma idan aka zuba ruwan zafi, ana iya maida shi kan wuta dan ya dahu sosai.
Mace kadai: Cokali uku a rana, a hada da zuma da madara (babban cokali).
Idan magidanci ne zai sha a sa cokali shida.
Ana iya sha safe da yamma domin samun kyakkyawa sakamako.
Allah ya sa albarka, ya kuma ba da lafiya da ingantacciyar rayuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp