Rahoton da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM), ta fitar ya bayyana cewa Isra’ila ta kashe Falasɗinawa sama da mutane 66,000 cikin shekaru biyu a yaƙin Gaza, wanda aka fara ranar 8 ga watan Oktoban 2023.
Rahoton ya ce mutane miliyan biyu daga cikin miliyan biyu da dubu ɗari sun tsere daga gidajensu saboda luguden wuta daga sama da ƙasa da Isra’ila ke kaiwa, wanda ya lalata kashi 90 cikin 100 na gidajen Gaza.
- Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
- Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni
Ma’aikatar Lafiya ta Hamas ta ce an jikkata mutane dubu 169, kuma kashi 80 cikin 100 daga cikin waɗanda aka kashe fararen hula ne ciki har da mata da yara.
Rahoton ya ƙara da cewa likitoci sama da 1000, da ’yan jarida 255, sun mutu yayin da asibitoci 38 da cibiyoyin lafiya 96 suka rushe, haka kuma motocin asibiti 197 sun ƙone.
Hukumomin ƙasa da ƙasa, ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya, sun ce adadin mutanen da suka mutu na iya wuce waɗannan alƙaluman.
Tun bayan harin 7 ga watan Oktoba, 2023, da mayaƙan Hamas suka kai wa Isra’ila wanda ya hallaka sojoji sama da 60 , Isra’ila ta fara luguden wuta a Gaza.
Tun daga wannan lokacin, yankin ya zama wurin tashin hankali da yunwa, inda mutane da dama ke mutuwa a kowace rana.














