Sanata Orji Uzor Kalu, mai wakiltar Abia ta Arewa, ya bayyana kansa a matsayin mafi shaharar ɗan siyasa daga yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.
Ya yi watsi da duk wani kwatance tsakaninsa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi.
- Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
- Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
Da yake magana a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a daren ranar Laraba, Kalu ya ce ba zai tattauna kan Obi ba sai idan an gayyace su duka biyu a tattauna da su kai-tsaye.
“Ni ɗan jam’iyyar APC, kuma ba na son yin magana a kan Peter Obi,” in ji shi.
“Ba don wani dalili na musamman ba, amma kawai ba na son yin magana a kansa. Idan tambaya ce ta shafi jagoran jam’iyyata, zan amsa.”
Lokacin da mai gabatar da shirin, Seun Okinbaloye, ya tambaye shi ko ya damu saboda yawancin ‘yan ƙabilar Ibo na goyon bayan Obi, Kalu ya cd, “A’a, kawai ban son yin magana a kansa.
“Idan kana son na tattauna a kan Peter Obi, to ka gayyace mu duka mu biyun mu zauna a tattauna ta awa biyu; kai za ka zauna a tsakiya, shi a gefe ɗaya, ni kuma a ɗaya gefen. Sai mu tattauna.”
“Peter Obi ba jagorana ba ne. Ni ne ɗan siyasa mafi shahara daga yankin Kudu maso Gabas. Na taɓa lashe jihohi biyu a ƙarƙashin jam’iyyar PPA, kuma na taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa.
“Kuri’u na miliyan 4.9 na samu a shekarar 2007 har yanzu suna nan. Jam’iyyata ta samar da ministoci da jakadu. Kowa na iya tsayawa takarar shugaban ƙasa, amma a tambaye ni kan abin da ya shafe ni, ba shi ba.”














