Rundunar ƴansanda ta Jihar Kano ta ce ta ceto mutane uku da aka sace a yayin wani aiki biyu da ta gudanar a Kano da Kaduna, tare da ƙwato babur da wasu shaidu. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a.
A cewar Kiyawa, a ranar 7 ga Oktobar 2025, rundunar daƙile garkuwa da mutane (Anti-Kidnapping) tare da tawagar sa-ido daga ofishin ƴansanda na Bebeji sun gudanar da sumame bayan samun bayanan sirri kan wani mutum da ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane. Wanda aka sace, Abdul Hamid Bello, mai shekaru 21, ya taimaka wajen kai jami’an tsaro inda aka ceto wani mutum mai suna Musa Idris, mai shekaru 65, a Saya-Saya, Ikara LGA ta Kaduna, yayin da masu garkuwar suka tsere.
- Ma’aikatan Jinya Sun Yaba Wa Gwamnatin Kaduna Kan Aiwatar Da Sabon Tsarin Albashi
- ‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar
A wani sumame daban, rundunar ta ce a ranar 9 ga Oktoba 2025, ta kuma ceto wani matashi, Ashiru Murtala, mai shekaru 19, wanda aka sace daga Beli, a ƙaramar hukumar Rogo da ke Kano, a ranar 5 ga Oktoba. An same shi a gonar rake a Hunkuyi da ke ƙaramar hukumar Kudan ta Kaduna bayan masu garkuwar sun gudu.
Kwamishinan Ƴansanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umurci a bai wa waɗanda aka ceto kulawar likita tare da ci gaba da bincike domin kama waɗanda ke da hannu a garkuwar.