Gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke, ya nanata kudurin gwamnatinsa wajen tallafa wa matan jihar, inda gwamnatin karkashin shirin aikin noma, ta dauki nauyin horas da mata 500 dabarun noma da takin gargajiya.
A jawabin da ya gabatar bayan kammala bayar da horon, wanda gidauniyar bunkasa aikin noma ta ‘Springtime Debelopment Foundation’ ta aiwatar, Adeleke ya jaddada aniyar gwamnatin tasa wajen tallafa wa matan jihar.
- Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe
- Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya
Gwaman, wanda kwamishinan kula da harkokin mata da yara ta jihar, Madam Ayobola Fadeyi-Awolowo ta wakilce shi a wajen kammala bayar da horon ya bayyana cewa, tun bayan ya zama gwamnan jihar, daya daga cikin kudurorin gwamnatin tsa shi ne, na tallafa wa rayuwar matan jihar.
Wadanda suka amfana da horon, an ba su horon ne a fannoni daban-daban da suka hada da yin noma da takin gargajiya da kuma yin noman kayan lambu da sauransu.
Kajin gidan gona da tare da kuma tallafa masu da kayan aikin noma.
Bisa tsarin wannan haron, kowace mace daya da ta amfana da horon, an ba su tallafin Naira Naira 50,000.
Kazalika, Adeleke ya danganta wannan tallafin kudin a matsayin mayar da hankalin gwamnatinsa na taimaka wa matan jihar.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmcin tallafa wa mata, wanda ya sanar da cewa; hakan na da muhimanci domin inganta gobensu.
Shi kuma shugaban gidauniyar, Dakta Deji Adeleke a nasa jawabin ya bayyana cewa, shirin wanda aka yi masa lakabi da ‘Beronica Adeleke’, manufarsa ita ce domin habaka tattalin arzikin mata don su zamo masu dogaro da kansu.
Shugaban, wanda mataimakinsa Banji Adesuyi, ya wakilce shi a wajen kammala bayar da horon ya bayyana cewa, shirin sabon aiki ne da aka kirkiro da shi a jihar.
Ya sanar da cewa, wadanda suka amfana an zabo su ne daga kananan hukumomin jihar 30, inda ya kara da cewa; mata 500 da suka amfana su ne rukunin farko, amma tun da farko gidauniyar ta tsara horar da mata 1,000 ne.