Sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa a majalisar dattawanl, Dr. Sama’ila Dahuwa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, yana mai bayyana rikicin cikin gida da rashin daidaito a shugabancin jam’iyyar a matsayin dalilin barinsa.
Dr. Dahuwa, wanda aka zaba a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya taɓa rike muƙamin kwamishinan lafiya a wa’adin farko na Gwamna Bala Mohammed. Ya bayyana ficewarsa ne a cikin wata wasika da ya rattaɓa wa hannu da kansa a ranar 6 ga Oktoba, 2025, wacce aka aike wa shugaban PDP na Tsakuwa, mazaɓar Kofar Gabar l, Azare, da ke ƙaramar hukumar Katagum.
- Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano
- Arewa Ta Daina Zama Ci-Ma Zaune A Tattalin Arziƙi – Gwamnan Bauchi
A cewar wasiƙar, “Yawaitar saɓani da rabuwar kai a cikin jam’iyyar PDP na kawo cikas ga yadda zan iya sauke nauyin da al’umma suka ɗora min a majalisar dattawa.”
Sanatan ya ce, bisa wannan dalili, ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP da gaggawa, yana mai tabbatar wa jama’ar Bauchi ta Arewa cewa zai ci gaba da wakiltar su yadda ya dace tare da kare muradunsu a majalisar dattawa.