Shugaban Gwamnonin Jam’iyyar PDP (PDP Governors Forum) kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa barin jam’iyya saboda wasu mutane alamar rashin jarumta ce. Ya ce duk wanda ya bar PDP saboda matsalar cikin gida hakan na nuni da gaza jurewa gwagwarmaya ta siyasa.
Gwamna Mohammed ya kuma tabbatar da cewa babban taron gangamin jam’iyyar na ƙasa (National Convention) da za a gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 ga Nuwamba, zai gudana kamar yadda aka tsara duk da ƙalubalen da ake fuskanta. Ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da kwamiti na taron jam’iyyar.
- Arewa Ta Daina Zama Ci-Ma Zaune A Tattalin Arziƙi – Gwamnan Bauchi
- Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, zai sanar da barin PDP a ranar Talata mai zuwa, yayin da ake hasashen Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, da Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ma na iya bin sahu. A baya, Gwamnonin Akwa Ibom da Delta, Umo Eno da Sheriff Oborevwori, sun bar jam’iyyar.7
Gwamna Mohammed ya jaddada cewa mambobin PDP su kasance masu ƙwarin guiwa, su guji damuwa da ficewar wasu daga cikin jam’iyyar. “Abin da ke nuna jarumta shi ne kasancewa da jam’iyya don a fuskanci ƙalubale. Barin jam’iyya saboda mutum ɗaya ko mace ɗaya ba jarumta ba ce,” in ji shi
Ya kuma sha alwashin cewa babban taron jam’iyyar zai gudana kamar yadda aka tsara, yana mai cewa, “Mun sha wahala a jam’iyya amma muna daurewa. Ba wanda zai hana wannan taro gudana. Idan magauta suka ci nasara akan PDP, to Nijeriya gaba ɗaya ta shiga duhu.” Gwamnan ya kuma caccaki gwamnatin APC, yana cewa tun bayan da PDP ta bar mulki a 2015, Nijeriya ba ta sake samun nagartacciyar gwamnati ba.