Jama’a, a yau a cikin shirin “Labarin Xinjiang A Zane” zamu ga yadda harkokin yawon shakatawa ke bunkasa a Xinjiang.
Aydarbek Birey makiyayi ne dan kabilar Kazak mai shekaru 36 wanda ke rayuwa a jihar Xinjiang. A da, Aydarbek Birey ya sha wahalar kiwon dabbobi, musamman idan dusar kankara ta afka musu. Yaya kuma rayuwarsa take yanzu?
- Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang
- Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako
“Tafkin Sayram yana ta kara janyo baki masu yawon shakatawa. Yanzu haka a kowace shekara ina samun karin kudi da ya kai kusan RMB Yuan 50,000 kwatankwacin fiye da dala dubu 7.” In ji Aydarbek Birey. Ya ce, a cikin ’yan shekarun nan, da taimakon gwamnati, ya zama ma’aikaci a ayarin dawaki a bakin tafkin Sayram, matakin da ya sa ya fara samun kudi ta sha’anin yawon shakatawa, tare da jin dadin rayuwarsa.
A hakila, sha’anin yawon shakatawa na fadada hanyoyin samun kudi ga mutanen Xinjiang.
Alkaluman da hukumar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta Xinjiang ta samar sun shaida cewa, a yayin hutun bikin murnar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a kwanakin baya, yankin ya karbi baki masu yawon shakatawa sama da miliyan 18, adadin da ya karu da kashi 11.26% idan aka kwatanta da na bara, kudin da bakin suka kashe ya kai fiye da Yuan biliyan 25, kwatankwacin dalar Amurka sama da biliyan 3.5, wanda kuma ya karu da kashi 11.71%. Hakan ya nuna cewa, aikin yawon shakatawa na Xinjiang yana da makoma mai kyau.
A watan Mayu na wannan shekara, an fitar da “Shirin raya sana’o’in al’adu da yawon shakatawa na Xinjiang (2025-2030)”, wanda ya gabatar da makoma mai haske a wadannan fannoni. Wato a cikin shekaru 6 masu zuwa, Xinjiang za ta dukufa a kan raya sana’o’in al’adu da wasanni da yawon shakatawa, wadanda za su shafi kudin Sin da yawansa ya wuce tiriliyan guda, kuma ana sa ran zuwa shekara ta 2030, adadin baki da yankin zai karba zai wuce miliyan 400 a shekara.
Bunkasar yawon shakatawa a Xinjiang wani bangare ne na ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na yankin. Hakan ya baiwa mutane kamar Birey damar kyautata zaman rayuwarsu, ya kuma fadada musu hanyoyin samun kudi. Muna da imanin cewa a nan gaba, karin mazauna yankin Xinjiang za su kara samun kudin shiga, tare da kara jin dadin rayuwarsu, kamar yadda malam Aydarbek Birey ya yi. (Mai zane da rubutu: MINA)