Jamiyyar PDP ta kasa ta yi wa dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shagube, inda ta ce, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ba zai taimaka masa a zaben 2023 ba.
Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a Abuja.
- Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Gana Da Jonathan, Ya Nemi Ya Mara Masa Baya
- Ganawar Tinubu Da Wike A Landan Ta Kada Hantar PDP
Sanarwar ta yi nuni da cewa, dan takarar mataimakin shugaban kasa ,Sanata Kashim Shettima da Bola Tinubu, ne kawai ke kokarin wanke kawunansu kan kurakuran da suka tabka wa ‘yan Nijeriya a baya.
Kokarin wanke kan ne yasa suke ta gudanar da ganawa da Jonathan don su janyo ra’ayinsa ya taimaka masu bayan alhali a zaben 2015 babu irin yarfen siyasa da basu yi wa Jonathan ba.
Ologunagba ya ce, ‘yan Nijeriya na cike da mamaki yadda Bole da wasu manya a jam’iyyar APC ke nesanta kansu da Gwamnatin shugaba, Muhammadu Buhari ba saboda ta gazawar gwamnatin.