Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya isa zauren Majalisar Dattawa a ranar Alhamis domin tantance shi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
An tsara gudanar da tantancewar a Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ke Abuja, a ƙarƙashin Kwamitin Majalisar Dattawa.
Farfesa Amupitan ya isa zauren majalisar da misalin ƙarfe 12:50 na rana, tare da Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, da wasu magoya bayansa.
Sanata Abubakar Lado, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin Majalisar Dattawa ne, ya jagorance su zuwa cikin zauren.
Da isarsu, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya tarbi Amupitan, tare da iyalansa da sauran baƙi, inda ya yi bayanin yadda tsarin tantancewar zai gudana.
An fara tantancewar da misalin ƙarfe 12:55 na rana, inda ake sa ran Farfesa Amupitan zai gabatar da tarihinsa da kuma amsa tambayoyin da ‘yan majalisar za su yi masa, kafin yanke shawara kan tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban INEC.














