Yayin da aka samu karuwa da matsalar tsaro data shafi kashe kashen da aka yi saboda lamarin Boko Haram, garkuwa da mutane, da kuma tashe- tashen hankula masu daure kai a wata daya daya gabata, a wasu sassan Nijeriya akwai kiraye- kirayen da aka yi na a aiwatar da dokar ta baci a Jihohin da abin ya shafa.
Sai dai kuma gwamnatin tarayya ta yi amfani ne da dokar ta baci a wasu lokutta domin ta samu damar kawo karshen matsalolin da suka yi sanadiyar samar da tashe- tashen hankula wadanda har suka sa wasu kungiyoyi daukar mataki da kansu wanda ba zai haifar da da mai ido ba, idan har aka bar su, suka kai ga yin hakan aka sa ido ana kallonsu Amma babbar tambayar anan yanzu ita ce wacce irin hanyar za’a yi amfani da ita, koma kuma wadanne hanyoyi ne za’a iya amfani da su domin a samu damar kawo kawo karshen matsalolin da suka yi sanadiyar samar da rikice- rikicen.
- Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara
- Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin
Akwai wuraren da aka samu matsololin na tashe- tashen hankula a Arewa maso yam Arewa maso gabas, da kuma Arewa ta tsakiya sai sashen Kudu maso gabashin Nijeriya da Jihohi kamar su Borno, Kebbi, Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kwara, Neja, Benuwe, da kuma Filato suna daga cikin Jihohin da ake samun irin matsalolin lokaci zuwa lokaci.
Wasu daga cikin manyan jami’an sojoji wadanda suka yi ritaya da kuma da masu rike da kambun mulkin yanzu da suka kasance a wurin kaddamar da littafin da tsohon Shugaban rundunar tsaro ta kasa, Janaral Lucky Irabor (ritaya) ya rubuta mai sunan, , ‘Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum,’ su a nasu ganin cewar lamarin aiwatar da dokar ta baci, ita ce hanya mafi dacewa da za ayi matsalar tsaro wadda ta shafi kasa.
Irabor shi a na shi ganin rashin karfin halin da za’a dauki matakin da yafi dacewa, shi yasa Nijeriya ta rasa matsayar daukar matakan da suka fi dacewa da matsalar tsaro da tashe- tashen hankulan da suka baibaye shi. Ya ce maganar kaddamar da dokar ta baci wanda majalisun kasa suke goyon baya ya isa ayi amfani da hakan wajen kawo karshen yake- yaken tada kayar baya da sauran matsalolin da suke hana ruwa gu da ruruta wutar tashe- tashen hankula.
Tsohon Shugaban rundunar tsaron a littafin, yace“Har yanzu gwamnati bata nuna alamun wata niyya ba ta yaki da kungiyar Boko Haram. Amma idan aka aiwatar da dokar ta bace tare da goyon bayan majalisun kasa biyu, ta hakan gwamnati ta samu dama ke nan ta samun dukkan abubuwan da suka daceda za su bata taimakon wajen samun nasarar tunkarar matsalar tsaro da samun nasara”.
Watan da ya gabata ne kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta yi kira da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da dokar ta baci a Arewacin Nijeriya,inda ta yi nuni tabarbarewar tsaro da ta sa aka yi asarar rayukan al’umma, da kuma durkushewar al’amuran da suke bunkasa tattalin arziki,da kawo ma kasa barazanar rashin zaman lafiya, da kuma hadin kai.
A jawabin da mai magana da yawun kungiyar, Farfesa. Abubakar Jiddere, ya ce kungiyar rashin jin dadinta akan abinda ta kira “yawan kai hare- haren da ake, garkuwa da mutane, da kashe- kashe” a sashen na Arewa, inda tace bai kamata gwamnati ta ci gaba da sa ido tana ganin abubuwan da basu kamata ba, suna faruwa ba tare da daukar mataki ba.
Kungiyar NEF ta lura da cewa abubuwan da za su taimaka domin kawo karshen lamarin tsaro basu isa ba, ana bukatarsu da yawa, ta wani bangaren kuma yin abubuwa ba kan ka’ida ban a rashin yinsu ko kuma ayi shiru, irin hakan shi zai sa abar su al’umma cikin rashin sani da ya dace su yi, har a kai ga ganin rashin ganin mutunci da yarda da duk wani abu na gwamnati, don haka ta yi gargadi da cewa muddin ba a daukin matakin da ya dace ba ganin yadda abubuwa suke kara tabarbarewa, mutane za su fara daukar “doka da hannunsu,” abinda idan ba sa’a aka yi ba ana iya shiga wani halin da bai kamata ba, har lamarin ya sa mulkin faral hula ya samu shiga babbar matsala da kuma gurgucewar zaman lafiya.
Masana tsaro da kungiyoyi sun bada goyon baya
Wata kungiya mai suna, mai suna matasan Kawara ta Kudu (KSYC) bada dadewa bane ta yi kira da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da cewa ya kafa dokar ta baci a Jihar Kwara saboda yadda lamarin tsaro ya muguwar lalacewa a Jihar.
A budaddiyar takardar da aka rubutawa Shugaban kasa mai dauke da sa hannun shugaban kauniyar, Dakta Oluwatobi Afolayan, KSYC, da kuma Mista Bashir Adejare, jami’in hulda da jama’a na kungiyar yace akwai al’ummomi da yawa, wadanda aka tilasta masu su koma wasu wurare saboda yawan kai hare- haren da ake yi .Koda yake akwai wasu da suke ganin da akwai wasu hanyoyin da za’a bullo ma lamarin.
A ganawar da yayi da Taibijin na Trust ritaya Manjo Janar U.I. Muhammed, mutumin da yayi ayyuka wurare daban- daban da suka fuskanci irin tashe- tashen hankulan a Nijeriya, yace: “Abin zabi ne.Lokacin da aka aiwatar da dokar ta baci a Jihohin sashen Arewa maso gabas uku da suka hada da (Borno, Yobe, da Adamawa), tabarbarewar tsaron ta ragu amma ba a kawo karshen shi ba.
“Akwai matsalolin da suka kamata ayi maganinsu.Na farko yadda ake ta hada- hadar mallakar kananan makami; domin kuwa da akwai milyoyi babu kuma wanda ya isa ya iya cewa ko nawa ne .Iyakokinmu da kasashe babu wani kwakkwaran tsaro: Nijeriya nada fadi da tsawon sikwaya kilmita 923,768 na iyakokinta da wasu kasashe ta fadi ta shi filin da kilomita 852 wanda fili ne, da kilomita na iyayokin ruwa da abin ya kai 4,047 gaba daya.Makamai suna zuwa ta hanyar jiragen ruwa da kuma dazuzzuka kowace rana. Idan aka aiwatar da dokar ta baci ya kuma kasance iyakokin Nijeriya basu da isasshen tasron da ya kamata, matakin daukar dokar ta baci ba zai yi wani amfani ba.
‘‘Muna bukatar kimniyya da fasaha a iyakokin kasashen da Nijeriya take da su, sai kuma ma’aikata masu kishin kasa wadanda za su hana shigowa da makamai. Ita ma fatara dole ne ayi maganin ta, domin tana da zumunci da tabarbarewar tsaro. Ya dace Gwamnatoci, su zuba a harkokin kasuwanci, sannan kuma wadanda suke da hali ya dace su zuba jari kan abubuwan da za su bunkasa rayuwar al’umma, ta hanyar taimaka masu kudaden yin sana’oi da dabaru na tafiyar da rayuwa ta hanyoyi daban- daban, da dabarun yinsu, ta haka sai a samu damar rage yawan mutane wadanda za’a ja ra’ayinsu wajen amfani da su aikata laifuka da suka shafi, tada zaune tsaye, garkuwa da mutane da kuma sauarn laifuka kamar yadda ya ce,”.
Tarihin Dokar ta baci a Nijeriya wadanda aka yi
A watan Mayu 1962, Firayim Minista na wancan lokacin Sir Abubakar Tafawa Balewa shin ne Shugaban kasa na farko wanda ya aiwatar da dokar ta baci, saboda kuwa ya dakatar da Firimiyan sashen yammacin Nijeriya, majalisar zartarwarsa, da kuma ‘yan majalisar, ya nada Dakta. Moses Majekodunmi a matsatin Kantoma.
Zamanin mulkin farar hula a jamhuriya ta biyu lokacin mulkin Shugaban kasa Shehu Usman Aliyu Shagari, Nijeriya ta fuskanci tarzomar yakin Maitatsine a Jihohi hudu da suka hada da Kano, Kaduna, Borno kuma Gongola. Daga karshe an samu galaba kansu wanda abin bai kai ga hakan ba wato dokar ta baci.Zamaninmulkin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo aka kara farfado da dokar ta baci a Jihar Filato a shekarar 2004 saboda barkewar rikici. Aka dakatar da Gwamna na wancan lokacin, Joshua Dariye bshi da ‘yan majalisarsa aka nada Janar Chris Alli (ritaya.) a matsayin Kantoma.
Daga sai Jihar ta biyo ma ta 2006 lokacin da gwamnan, Ayo Fayose shi da ‘yan majalisarsa ka dakatar da su aka nada ritaya Janar Tunji Olurin a matsayin Kantoma. Amma wancan ya bambanta da irin halin da ake ciki yanzu domin kuwa lokacin lamarin siyasa ne.
A watan Disamba, 2011, Shugaban kasa ma lokacin Goodluck Ebele Jonathan ya aiwaytar da dokar ta baci a Jihar Filato saboda rikicin kabilanci da addini. Hakanan ma a Jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa a watan Mayu 14, 2013. Amma fa, ya bar gwamnonin da ‘yan majalisun.
Wanda ba adade da yi ba shi ne na ranar 18 ga Maris 18 2025, lokacin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu y kaddamar da dokar ta baci a Jihar Ribas bayan da aka samu rikta- rikitar siyasa tsakanin Gwamna, mataimakinsa, da ‘yan malaisarsa ak adakatar da su, yayin da kuma aka nada ritaya Bice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, a matsayin Kantoma.
Mutane da yawa daga ciki har da, in kungiyoyi masu zaman kansu,gwamnoni, da sauran jagororin siyasa sun nuna rashin jin dadinsu, kan amincewa da kafa dokar ta baci a kowane lokaci, yayin da wasu kuma ai tsarin mulki ya ba Shugaban kasa dama idan aka yi la’akari da sashe na 305 na tsarin mulkin 1999.