Kwamitin Tallafa Wa Marayu na Kungiyar Izalatil Bidi’ah Wa’ikamatussnah (JIBWIS) FCT, ya gudanar da taron yaye iyaye mata 120 da aka koyar da su sana’o’i mabanbanta. Iyaye matan da aka mutu aka bar musu marayu an koyar da su nau’in sana’o’i 16.
A yayin gudanar da taron Darakta Janar Na Kungiya na Kasa Alhaji Ahmad Ibrahim Lau, wanda ya wakilci Shugaban kungiyar na kasa Shek Dakta Adbullahi Bala Lau, ya taya mahalarta taron murna da farin cikin hallararsu da fatan Allah ya albarkaci taron, sannan ya ja hankalin mahalarta taron da inda ya ba da misalin Shehu Dan Fodiyo, inda ya ce, shehun malamin ya ce, ku yi ilimi, kasuwanci da kiwo da kuma noma.
- FCT Ta Amince Da Naira Miliyan 8.2 Kan Kujerar Aikin Hajjin 2026
- Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul
Ya kara da cewa ita uwa ita ce makarantar farko ga abin da ta haifa, in ya tashi da hali mai ita ta koya masa, idan kuma aka samu akasi sakacinta ne, ya yi addu’ar Allah ya saka wa kowa da alheri.
Shi ma a nasa jawabin yayin gudanar da taron, shugaban kwamitin Alhaji Abdullahi Abdulmalik Digi, ya ce, a shekaru hudu da ya yi yana jagorancin kwamitin sun yi abin da yakamata su yi, inda ya ce, a Azumin bara an dauki yara marayu 2000 da aka raba musu abinci da suka hada da buhunan shinkafa da kuma kayan Sallah da za su dinka, mata aka raba musu shadda mata kuma atamfofi inda jimillar kudin da aka kashe ya zama Naira miliyan 64.2.
Bayan wannan an kashe Naira milin 26 wajen biya wa yara 520 kudin makaranta, inda kowane yaro ake biya masa Naira dubu 50 a kananan hukumomi shida na FCT Abuja.
Sannan an kashe Naira miliyan 3 wajen taimakawa wasu da suka yi wa kwamitin hidima da suka rasu da kuma wadanda a yanzu ba su da lafiya, inda aka aika wa kowannensu Naira dubu hamsin-hamsin har gida.
Ya kara da cewa a wannan taro kuma, mata ne iyayen marayu su 120 aka koyawa sana’o’i, inda aka dauki kusana makonni uku ana koyar da su domin su samu ikon rike marayun da aka mutu aka bar musu. A wannan aiki na koyarwa an kashe Naira miliyan 4.675, a wurin sayen kayan aikin koyar da su da kuma zirga-zirga. Kananan hukumomin guda shida su ma sun kawo ta su gudunmawar ta Naira miliyan 2.4, suka idan an kammala basu horon kowacce a ba ta Naira 20,000 su rike kamar jari, jimillar kudin da kashe a wannan ba da horo na sati uku, ya kama Naira miliyan 7.75.
Jimillar abin da kwamitin ya kashe tun daga watan Azumin bara tun daga miliyan 66.2 kawo yanzu, an kashe Naira miliyan dari da dubu dariyu da saba’in da biyar N1.275 a shekarar bana kadai