Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta samu kashi 95 na kuri’un da aka kada a zaben 2027.
Gwamna Sani ya yi karin haske da cewa, jam’iyyar APC tana da ‘yan majalisar wakilai hudu ne kawai a shekarar 2023, inda ya bayyana cewa jam’iyyar a yanzu tana da mambobi goma sha uku (13) a zauren majalisar.
Da yake jawabi ga wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a babban taron gangamin da aka gudanar a Kaduna a karshen mako, Gwamna Sani ya ce, biyo bayan sauya sheka zuwa APC, a yanzu APC na da ‘yan majalisar wakilai 13 daga jihar Kaduna, inda jam’iyyar adawa ta PDP ke da uku kacal.
Ya kara da cewa, a majalisar dokoki ta jihar, APC ce ke da rinjaye da mambobi 26 inda PDP ke da mambobi takwas kacal.