Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP bisa zargin rashin cika alkawuran da aka daukar masa.
Ya kara da cewa shi ba zai taba zama a wurin da ba adalci da mutunci ba. Mai taimaka wa Shekarau a kafafen sadarwa, Bello Muhammad Sharada ne ya tabbatar da haka, inda ya ce Shekarau ya fita daga NNPP kuma ya ajiye takarar majalisar dattawa karkashin jam’iyyar.
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
- Tinubu: Jonathan Ba Zai Kubutar Da Kai A Zaben 2023 Ba —PDP
Ya kuma aika wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) cewa ba zai yi wannan takara ba, sannan ya ce jama’a su sani ko mai za a fada a kansa, ba zai zauna a gurin da babu adalci da kuma martaba da aminci ba.
A safiyar ranar Litinin da ta gabata ce, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar tare da shugabanni da jiga-jigan PDP suka dira fadar Mundabawa ta Shekarau, domin karbarsa cikin jam’iyyar PDP.
Rade-radin da aka jima ana yi tun bayan da ya bayyana dangantaka tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ta yi tsamiya.
Da alama dai hasashen da ake na cewa kujerar sanatan Kano ta tsakiya ba a maimaitawa zai iya tabbata, domin tun daga shekara ta 1999 har zuwa yau ba wani sanata daga Kano ta tsakiya da ya jera zango biyu a kan wannan kujera.
Dama an yi zaton Malam Ibrahim Shekarau zai iya karya wannan tarihin kamar yadda ya karya na kujerar gwamna, wanda shi ne gwamnan farar hula na farko da aka taba samu ya yi zango biyu a kan kujerar gwamnan Jihar Kano.