Indomie wata taliya ce mai dadi ci a baki ba tare da wahalar taunawa ba. Bugu da kari ta samu karbuwa ga al’ummar Nijeriya da ma sauran kasashen duniya.
Abinci ne da ake sarrafa shi ta hanya daban-daban, ana soya taliyar Indomie a ci kamar waina, ana dafa ta a ci haka ba tare da komai ba domin a cikinta an hada duk wasu sinadarai da suke dandanon farfesu, sannan jikata a ci da ruwan sanyi, ana zuba mata ruwan dumi a cinye.
Idan mutum yana jin yunwa kuma babu abinci a kusa da shi ko kuma ba zai iya jure zaman dafa abinci ba, to zai iya daukar Indomie ko babu ya ci ba tare da ya sarrafa ta ba, sannan ana dafa ta a soya kwai a dora a samanta a ci.
A duk nau’in abincin da muke sarrafawa mu ci babu wanda ya kai taliayar Indomie saukin sarrafawa.
A jikinta akwai sinadarai masu sanya abinci armashi ga dandanon mai gamsarwa. Da taliyar Indomie ce ake rarrashin yaran da za su tafi makaranta ta hanyar dafa musu a sanya a mazubi su tafi makaranta domin in an fito cin abinci su ci.
Ba yara kadai ba hatta manyan mutane Maza da Mata musamman masu ‘ya’ya suna matukar amfani da ita, sannan ba kawai abincin masu kudi ba ce, hatta talakawa suna sukunin sayenta su ci.
Haka zalika ana iya ajiye ita wannan taliyar Indomie ta jima ba ta lalace ba, tana nau’i daban-daban na dandanon, misalin: akwai mai dandanon yaji, akwai mara yaji, akwai mai dandanon naman kaza.
Sannan kuma girma-girma ce, akwai ta cikin babban mazubi (Hungry Man), akwai ta matsakaici mazubi (Medium size), sannan (Small size).
Bincike ya nuna cewa, indomie ya matukar karbuwa a wuraren masu sana’ar Shayi a biranen kasar nan, inda zaka ga mutane na zuwa wajen sayar da shayi ana hada musu indomie da kwai ko kuma a hada musu da nama ko kifin gwangwani.
Al’umma da dama na amfani da Indomie a gidajensu ana kuma tanadarwa ga yara ‘yan makaranta don amfanin su.
‘’Ina matukar jin dadin amfani da indomie a harkoki na nay au da kullum, kuma ina jin dadin haka, ina kuma kira ga iyaye mata da magidanta da su rungumi amfani da Indomie” in ji wata matar aure da ta bukaci a sakaya sunanta.