Wani matashi mai suna Auwalu Muhammad ya kwaƙule idanuwan ƙannuwarsa ‘yar shekara bakwai a duniya, Rukayya Muhammad, domin yin tsafin neman kuɗi a yunƙurinsa na zama hamshaƙin mai kuɗi.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Boka mai bayar da sa’ar yin kuɗi da ke sanya jama’a ciro sassan jikin mutane kamar idanu da azzakari ya nemi Auwalu da ya ciro idanun yarinyar domin a masa tsafi ya zama mai kuɗi dare guda.
- Don Nuna Wa Duniya Kyawawan Al’adunmu Na Kirkiri Manhajar ‘Unlock Arewa’ – Bappi
- Don Nuna Wa Duniya Kyawawan Al’adunmu Na Kirkiri Manhajar ‘Unlock Arewa’ – Bappi
A halin yanzu likita ya tabbatar da cewar Rukayya ba za ta sake gani ba domin idanuwanta sun lalace gaba ɗaya.
Wannan abun takaici ya faru ne a yankin Wailo da ke ƙaramar hukumar Ganjuwa a jihar Bauchi.
A lokacin da ake zantawa da mahaifin yarinyar ya bayyana cewar wanda ake zargin (Auwalu) ya yaudari ‘yar uwar tasa, wacce suke da iyaye guda tare, zuwa daji tare da kwaƙule mata idanu da ƙarfin tsiya.
Mahaifin Rukayya, Muhammad Adamu mazaunin ƙauyen Bayan Dutse da ke Wailo, a gundumar Kubi cikin ƙaramar hukumar Ganjuwa a ranar 17 ga watan Oktoba ya kai rahoton caji ofis ɗin Soro ya ke shaida cewar wani matashi mai suna Auwal Dahiru mai shekara 17, ya kai farmaƙi wa yarsa da ƙoƙarin kasheta da kwaƙule mata idanuwanta.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil a ranar Litinin, ya ce, lokacin da ‘yansanda suka samu rahoton faruwar lamarin cikin gaggawa a ƙarƙashin Baturen ɗansanda da ke kula da caji ofis ɗin Soro, CSP Aliyu Mohammad Goni, sun kai agaji inda lamarin ya faru.
A lokacin da aka ɗauki Rukayya zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi, domin mata jinya, kwararren likitan Ido a asibitin ya tabbatar da cewar yarinyar ba za ta sake gani da idanuwanta ba har ƙarshen rayuwarta.
Kan haka ne rundunar ‘yansandan ta ce zuwa yanzu ta cafke mutane shida da ake zargi da hannu kan wannan aika-aikar waɗanda suka haɗa da Auwal Dahiru, mai shekara 17 da ke Bayan Dutse, Wailo, Kubi, Ganjuwa, Mohammed Rabiu (mai shekaru 19), Saleh Ibrahim (20), Nasiru Muhammad mazaunin cikin garin Soro a Ganjuwa, Hassan Garba mazaunin Soro da kuma Garba Dahiru mai shekara 43 a duniya kuma mazaunin Soro.
“Lokacin da ake bincike, waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu,” Wakil ya tabbatar.
Jami’in watsa labaran ‘yansandan ya kuma sanar da cewa yanzu haka bincike na ci gaba da gudana domin zaƙulo dukkanin masu hannu a wannan aikin domin su fuskanci Shari’a.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, State Command, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umarci a gaggauta maida binciken kes ɗin zuwa sashin binciken manyan laifukan (SCID), Bauchi domin faɗaɗa bincike da gano wasu abubuwan da suke akwai kan lamarin.
Ya bayar da tabbacin wanzar da gaskiya da adalci kan lamarin da yin aiki bisa kwarewa.













