Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauye-sauye a shugabancin hafsoshin tsaron Nijeriya.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sunday Dare, mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, ya fitar a ranar 24 ga watan Oktoba, 2025.
- Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi
- Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa
A cewar sanarwar, Janar Olufemi Oluyede shi ne sabon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, wanda ya maye gurbin Janar Christopher Musa.
Haka kuma an naɗa Manjo Janar W. Shaibu a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Air Vice Marshal S.K. Aneke a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Sama, da Rear Admiral I. Abbas a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Ruwa.
Manjo Janar E.A.P. Undiendeye zai ci gaba da rike mukaminsa na Shugaban Sashen Leken Asirin Tsaro (Defence Intelligence).
Shugaba Tinubu, ya gode wa tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, da sauran tsoffin hafsoshin bisa gudunmawar da suka bayar.
Ya kuma bukaci sabbin hafsoshin da su tabbatar sun cancanci nadin da aka musu ta hanyar nuna ƙwarewa, haɗin kai wajen tsaron Nijeriya.
“Shugaban ƙasa ya bukaci sabbin hafsoshin tsaro da su tabbatar da cewa sun cancanci nadin da aka musu ta hanyar nuna ƙwarewa, faɗakarwa, da zumunci wajen tsaron ƙasa,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta bayyana cewa dukkanin sabbin naɗin za su fara aiki nan take.













