Assalamu Alaikum. Jama,a masu bibiyarmu a wannan shafi na Girki Adon Mata, bayan gaisuwa irin ta Addinin Musulunci.
Girkimmu a wannan makon shi ne, za mu bayyana yadda ake yin Kosai Mai hade-hade.
- …Dalla-dallar Yadda Aka Kashe Kudin Tallafin Mai
- Kasar Sin Ta Sake Bayyana Matsayinta Kan Rahoton Ofishin OHCHR Dangane Da Jihar Xinjiang
Abubuwan da yakamata uwargida ta tanada: Wake rabin kwano, Maggi, Gishiri, Kayan kamshi, Man gyada, Attarugu da albasa, Cabbege, Tattasai, kuri.
Da farko za ki wanke wakenki ki cire hancin ya fita tas sai ki jika shi ki barshi ya jiku, Idan ya jika sai ki markade shi, idan aka markada sai ki zuba maggi da gishiri da kayan kamshi kuri duka, sai ki gurze cabbage din ki ki zuba ki jajjaga attaruhu da tattasai ki zuba sannan ki yayyanka albasa kanana itama ki zuba a ciki ki gauraya sai ki dauko ludayi mai kyau babba sai ki ta bugawa, ya bugu sosai a nan sai ki dora manki a wuta.
Idan ya yi zafi, sai ki sa karamin ludayinki ki ko cokali kina diba ki na sawa a manki kadan-kadan kamar de yadda na kosai yake sai kina sawa a mai ya soyu sosai ya yi ja kamar kosai haka za kiyi har ki gama.
Amma fa ki tabbatar kina yi kina bugawa, in baki iya yi ba ki gwada, Allah ya taimaka.