A kokarinsa na saukaka wa kwastamominsa hada-hada da mu’amalar banki a duk inda suke, Bankin Taj da aka fi sani da ‘TajBank’ zai kaddamar da manhajar mu’amalar banki ta kashin kansa ba da jimawa ba.
Manhajar dai za ta kara kawo wa bankin kwastamomi da kara bunkasa ayyukansa a fadin Nijeriya.
- Malam Ina So A Taimaka Mun Da Maganin Damuwa Da Bakin Ciki?
- Jami’an Kashe Gobara Sun Ceto Mutum 91 Da Dukiyar Da Ta Kai Kusan Naira Miliyan 25 A Kano
Manajan Daraktan Bankin na Taj, Alhaji Hamid Joda ya bayyana haka yayin da mahukuntan Kamfanin Media Trust suka ziyarce shi a Abuja.
A ta bakinsa, “Muna shirin kaddamar da Bankinmu mai amfani da fasahar sadarwar zamani irinsa na farko a duk fadin Nijeriya kuma tsarin banki ne da wasu matasa ‘yan Nijeriya suka samar a nan cikin gida.
Yana kunshe da abubuwa daban-daban da zai iya gogayya da kafada da kafada da sauran ire-irensa na kasashen duniya.
Muna sa rai mu kaddamar da shi ga jama’a cikin watan Satumba ko Oktobar nan mai zuwa, kasancewar muna jiran kammala wasu sharudda da samun amincewa.
Bankin na zamani an tsara shi ne musamman domin shigo da matasa cikin harkar banki kuma muna bukatar ‘yan jarida su yada labarinsa”.
Alhaji Joda ya kara da cewa bankin na Taj ya samu gagarumar nasara a kasuwar Nijeriya duk da kalubalen da aka fuskanta na annobar cutar Korona.
“2019 ta kasance shekarar da aka dan sha wuya saboda kalubalen annobar Korona.
Dama tun a farkon shekarar an sha wuya amma Alhamdu Lillah, mun samu nasarar magance kalubalen da aka fuskanta har aka samu riba cikin wata takwas da kafuwa.
Baya ga haka, mun samu nasarar biyan kudaden gudanar da ayyukanmu a shekarar farko ta fara kasuwanci kuma muka ci riba duk dai a shekarar ta farko wanda ba a saba ganin hakan ba a bangaren hada-hadar bankuna.”
Wakazalika ya kara da cewa bankin ya yi nasarar kara yawan jarin hada-hadarsa daga Naira Biliyan 50 zuwa Naira Biliyan 140.
Haka nan ya ce ba da jimawa ba TajBank zai kaddamar da Shirin Lamuni na SUKUK na Naira Biliyan 100.