A halin yanzu, ana gudanar da bikin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na shekarar 2022 wato CIFTIS a takaice a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
A bana, akwai kasashe da kungiyoyin kasa da kasa guda 71 da suka kafa shagunan nune-nune ko shirya taruka a wajen bikin na wannan karo.
Ciki har da kasashe guda 10 da suka hada da kasar Switzerland, da Burundi, da haddadiyar daular Larabawa da sauransu, wadanda a karo na farko, suka kafa shagunan nune-nune a yayin bikin CIFTIS da sunayen kasashensu.
Jami’in sashen kula da harkokin tattalin arziki na ofishin jakadancin haddadiyar daular Larabawa dake nan kasar Sin, Saeed Alghfeli ya bayyana cewa, bikin CIFTIS ya kasance daya daga cikin muhimman dandaloli guda uku, dake bayyana yadda kasar Sin take bude kofarta ga ketare.
Kuma a yayin bikin na wannan karo, kasarsa na fatan gabatar da karin bayanai game da tattalin arzikinta ga masu zuba jari na kasar Sin.
A yayin wannan biki, a karo na farko, Italiya ta kafa wani shagon nune-nune da sunanta. Wakilin ofishin birnin Beijing na kwamitin cinikin waje na kasar Italiya Gianpaolo Bruno ya bayyana fatan samun karin abokan hadin gwiwa a yayin wannan biki.
Kasar Cyprus tana yankin iyaka dake tsakanin nahiyar Turai, da ta Asiya, da ma ta Afirka. Minista mai kula da harkokin tattalin arziki da ciniki na ofishin jakadancin kasar Cyprus dake kasar Sin Petrou Petros ya ce, a karo na farko, kasarsa ta kafa shagon nune-nune a yayin bikin CIFTIS da sunanta, domin tana fatan gabatar wa karin abokai na kasar Sin, sana’ar hidimomi da ke akwai a kasar Cyprus.
Cikin shekaru 10 da suka gabata, darajar hidimomin da kasar Sin ta shigo daga ketare ta zarce dallar Amurka triliyan 4.
A matsayin wani muhimmin bikin baje koli na kasa, bikin CIFTIS ya samar da damamaki masu dimbin yawa daga dukkan fannoni ga kamfanonin kasashen duniya, domin su shiga manyan kasuwannin kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)