Tattaunawar Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i (ASUU) ta kara zurfafa, inda aka fara sakin Naira biliyan 2.3 ga jami’o’i a fadin kasar a matsayin wani bangare na kokarin magance matsalolin jin dadi da walwalar Malamai a fannin ilimin manyan makarantu.
Ministan Ilimi, Dr. Maruf Olatunji Alausa, ya bayyana cewa, Naira biliyan 2.311 da aka fara fitarwa, yana matsayin albashin rukuni na 8 ne da kuma basussukan kudin karin girma ga ma’aikatan jami’a.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Folasade Boriowo ya fitar ranar Laraba a Abuja.
Dr. Alausa ya ce, za a fitar da kudaden ne ta Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), wanda hakan ke nuna kudirin Shugaba Bola Tinubu na biyan basussukan da ya gada domin karfafa kwarin gwiwar ma’aikata a manyan makarantu.














