A wani babban sauyi na siyasa da ya faru a ranar Alhamis, ƴan majalisar wakilai shida ne suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar APC yayin zaman majalisar. Wannan ya faru ne a gaban shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da kuma gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, wanda shi ma kwanan nan ya koma APC.
Cikin waɗanda suka sauya shekar akwai ‘yan majalisa biyar daga jihar Enugu da suka bar jam’iyyar PDP — Obetta Chidi, da Anayo Onwuegbu, da Dennis Agbo, da Martins Oke, da Nnolim Nnaji — tare da Daniel Asama daga jihar Filato wanda ya bar jam’iyyar Labour Party (LP). Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ya karanta wasiƙunsu sannan ya taya su murna bisa matakin da suka ɗauka.
- Rikicin Yelwa: Gwamnan Bauchi Ya Gargadi Masu Kokarin Janyo Tashin Hankali A Jihar
- Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa
‘Yan majalisan sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da rashin daidaito a jam’iyyunsu ne ya sa suka yanke shawarar komawa APC. Kakakin majalisar ya yaba da matakin nasu yana mai cewa sun ɗauki “hanya madaidaiciya” wadda za ta ƙarfafa jam’iyyar mai mulki a majalisar.
“Kuna da cikakkiyar dama da kuka shiga jam’iyyar APC. Muna maraba da ku cikin iyalin jam’iyyar,” in ji Kakakin Abbas, yayin da mambobi da dama suka yi tafi.
Sauyin shekan ya kara nuna karfi da tasirin APC musamman a yankin Kudu maso Gabas, bayan gwamnan Enugu Peter Mbah ya bar PDP zuwa APC makonni kadan da suka gabata. Masana harkokin siyasa na ganin wannan ci gaban zai iya karfafa wa jam’iyyar mai mulki guiwa a shirye-shiryenta na zaben 2027.














