Rundunar ƴansandan Jihar Adamawa ta kama wani mutum mai suna Anas Dauda, mai shekara 32, ɗan unguwar Jalingo B a Lamorde Ward, ƙaramar hukumar Mubi ta Kudu, bisa tuhumar mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba.
Kamen nasa ya biyo bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, inda aka ganshi yana nuna bindigar AK-47 mai ɗauke da kwanson harsashi guda uku, yana yi wa jama’a barazana tare da iƙirarin cewa zai sayar ko ya bayar da hayar bindigar ga wanda ya nemi hakan. Wannan ya haifar da tsoro da firgici a cikin al’umma.
- An Nada Adamar Kamaye Sarautar Jakadiya A Kasar Ghana
- ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano
Bayan samun rahoton, ƴansanda sun tura jami’ai ƙarƙashin jagorancin DPO na Mubi ta kudu domin bibiyar lamarin, da bincika da kama wanda ake zargi. A cikin lokaci kaɗan, jami’an suka bi sahun sa suka kuma damƙe shi a wani yankin da ke nesa da Mubi.
Kwamishinan ƴansanda ya bayar da umarnin a miƙa lamarin ga sashin Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Yola domin gudanar da cikakken bincike da gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.
Mai magana da yawun rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da kama wanda ake zargin, yana mai cewa kwamishinan ƴansanda ya gargaɗi jama’a su guji duk wani aiyuka da za su iya tayar da hankalin jama’a ko karya doka, yana mai tabbatar da cewa rundunar ta dage wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.














