Dan takarar Majalisar Dattawa na Kano ta tsakiya. Dokta Abubakar Nuhu Danburam ya ce jam’iyyarsu ta PDP ita ce za ta kawo mafita daga matsalolin da jam’iyya mai mulki ta jefa al’ummar kasar nan.
Ya bayyana haka ne da ya ke zantawa da ‘yan jarida a Kano a lokacin da jam’yyar me karbar Sanata Shekarau da ya yi kome cikintan ranar Litinin.
- Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Keta Ka’idojin Fitar Da Kayayyaki
- Malam Ina So A Taimaka Mun Da Maganin Damuwa Da Bakin Ciki?
Danburam ya yi nuni da cewa kafin zuwan shugaban kasa Buhari kan karagar mulki ba irin abinda bai fada ba na nuna gazawar jam’iyyar PDP, hakan tasa al’ummar kasar nan suka yi masa kyakkyawan zato suka zabe shi wanda yanzu sun dawo suna da na sani.
Ya ce, yanzu komai ya sakwarkwace a kasar nan ga rashin tsaro da yawan hauhawar farashin kayan abinci ga faduwar darajar Naira ga kuma dinbim basussuka da ake ciyowa, harkar ilimi ya tabarbare malaman jami’a na yajin aiki.
Dakta Abubakar Nuhu ya ce a baya da PDP ke mulki duk babu irin wadannan matsalolin, mstsalar Boko Haram da aka samu a yankin Arewa ta Gabas an yi kokarin kau dashi lokacin Goodluck amma amma zuwan wannan Gwamnatin sai abin ya dada ta’azzara ya mamaye kusan jahohin Arewa ana kashe mutane da sace su Iowa na cikin fargaba.
Ya ce har Gwamnatin PDP ta gama mulki abinci baya gagarar bukatar talaka, amma yanzu buhun shinkafa da aka sayarwa a baya N7,000 yanzu ana saida buhu sama da N30,000 da kyar talaka ke iya ciyar da kansa.
Harkar ilimi ya tabarbare duk wani abu da jama’a za su sami sauki babu, don haka al’ummar kasar nan su baiwa takarar Atiku goyon baya wanda yana da manufofi da zai dawo da kasar nan cikin hayyacinta.
Dakta Abubakar Nuhu Danburan ya yi nuni da cewa dukkan ‘yan majalisun Dattawa da suka wakilci Kano ta tsakiya musammnan ma tsofaffin Gwamnoni ba abinda suka kawo mata na cigaba, sun yi zaman dumama kujera ne.
A matsayinsa na tsohon dan majalisar tarayya na karamar hukumar Birnin Kano kowa yasan irin rawar da ya taka wajen kawo kuduri da kuma gudanar da muhimman ayyuka na cigaba.
Wannan takara da yake na sanata a Kano ta tsakiya za ta zama alkhairi ga cigaban Kano da kasa baki daya.