Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sake fuskantar wani mummunan sakamako bayan ta sha kashi a hannun Enyimba United a wasan mako na 11 na gasar NPFL, wanda aka buga a filin wasa na Enyimba International Stadium da ke birnin Aba, jihar Abia.
Ɗan wasan Enyimba, Bassey John, ne ya fara zura ƙwallo a ragar Pillars a minti na 27, kafin Edidiong ya ƙara ta biyu mintuna kaɗan kafin a tafi hutun rabin lokaci. Wannan ya nuna ƙarara cewa masu masaukin baƙi sun fi ƙarfin Pillars a wasan.
Sakamakon ya baiwa Enyimba damar hawa zuwa matsayi na 6 a teburin gasar da maki 16 daga wasanni 11, yayin da Sai Masu Gida suka sake komawa matsayi na 20, wato a ƙarshen teburin. Wannan na nuni da cewa ƙungiyar ta Kano Pillars tana cikin hali mai tsanani a wannan kakar wasa.
Duk da cewa an sauya mai horaswa a makon jiya, sabon kocin ƙungiyar, Mohammed Babaganaru, bai samu nasarar ɗaukar maki ko ɗaya ba tun bayan karɓar ragamar horar da Pillars. Wannan ya sanya magoya bayan ƙungiyar cikin damuwa, suna tambayar ko ƙungiyar za ta iya guje wa fita daga Firimiya a wannan kakar.
Masu sharhi kan harkokin ƙwallon ƙafa na ganin cewa rashin daidaituwar tsaron baya da rashin ƙwarewar ƴan wasan gaba wajen cin ƙwallo ne ke ci gaba da jefa Pillars cikin wannan halin. Duk da haka, akwai fatan cewa sabon kocin zai iya samo mafita kafin lamarin ya kai ga faɗawa rukunin ƴan dagaji.














