Tsohon dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Pogba ya bayyana cewa yana fuskantar kwace da barazana daga wata kungiyar masu aikata laifi kamar yadda lauyansa ya tabbatar wa da jami’an tsaro.
Kamfanin Dillacin Labarai na AFP ya ambaci wata kafa da ke cewar ‘yan sandan Faransa sun fara bincike kan lamarin sai dai tun a baya dan uwan Pogba, Mathias ya fitar da wani faifan bidiyo a kafar sada zumunta da yin alkawarin zai wallafa ‘wasu bayanai masu girma kan tsohon dan wasan na Manchester United.
Mathias Pogba ya ce bayanan suna da girma, sai dai bai yi wani karin bayanai ba inda ya ce ana samun karin barazana da kokarin yi wa Pogba kwace daga wata kungiyar masu aikata laifi’ kamar yadda ya sanar.
Sai dai a cewarsa dan uwan na Pogba an sanar da jami’an tsaro a Italiya da na Faransa tun a watan jiya, amma ba wani karin bayani kan lamarin, bayan da ake yin bincike akan lamarin.
Pogba, wanda ya lashe kofin duniya da tawagar Faransa a shekarar 2018, ya koma Jubentus a kakar nan, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Manchester United wadda ta kashe fam miliyan 89 wajen sayansa a shekarar 2016.
A faifan bidiyon, Mathias Pogab ya ce ya kamata duniya da ‘yan uwa da magoya baya da tawagar Faransa da kungiyar Jubentus da kamfanonin da suke hulda da shi su san wasu batutuwan.