An samu taƙaddama a a zauren majalisar dattawa a ranar Talata lokacin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce “ba ya jin tsoron Trump.”
Lamarin ya faru ne yayin zaman da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ƙaryata wani rahoto da ya zarge shi da cewa ya mayar wa Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump da martani kan zargin kisan gillar Kiristoci a Nijeriya.
- Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma
- Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU
Akpabio ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da nufin tayae da hargitsi a tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce rahoton ya haɗa tsohon hoto da maganganu na ƙarya, inda ya bayyana cewa fadar shugaban ƙasa ce kaɗai ke da hurumin mayar da martani ga shugabannin ƙasashen waje.
“Na kai rahoton wannan labari ga ’yansanda da hukumar DSS,” in ji Akpabio, inda ya gargaɗi cewa yaɗa labaran ƙarya na iya haddasa rikici.
Sai dai Sanata Barau Jibrin ya ce, “Ni ɗan Nujeriya ne, kuma zan faɗi ra’ayina. Ba na jin tsoron Trump. Mu ƙasa ce mai cikakken ’yanci.”
Maganarsa ta sa wasu Sanatoci dariya kafin Akpabio ya rufe tattaunawar, inda ya roƙi ’yan jarida su tabbatar da sahihancin labarai kafin su wallafa.














