Gwamnatin tarayya ta amince da gina sabbin gidaje ga shugabannin manyan kotuna da kuma aiwatar da muhimman ayyukan ruwa da ci gaban tituna a babban birnin tarayya (FCT). Ministan FCT, Nyesom Wike, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a ranar Alhamis.
Wike ya bayyana cewa sabbin gidajen za a gina su ne domin Shugaban Kotun ɗaukaka ƙara (Court of Appeal), Shugaban Kotun Ma’aikata ta Ƙasa (National Industrial Court), da babban alƙalin Kotun Tarayya (Federal High Court), da kuma babban alƙalin kotun FCT (FCT High Court). Ya ce wannan mataki na cikin ƙoƙarin gwamnati na samar da muhallin da ya dace ga manyan jami’an shari’a domin sauƙaƙa aiyukansu.
- Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja
- Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe
A ɓangaren aiyukan ruwa, Wike ya bayyana cewa majalisar ta amince da aikin samar da ruwan sha ga yankunan Karu, da Karshi, da Orozo da Bwari, wanda ya kasance ci gaban shirin samar da ruwa na birnin tarayya (Greater Abuja Water Supply Project). Ya ce tuni an fara kuma ana sa ran kammala shi kafin watan Mayu na shekara mai zuwa. “Shugaban ƙasa ya sha alwashin cewa ruwan Abuja zai isa ƙananan yankuna, kuma mun riga mun ƙaddamar da wannan aiki,” in ji Wike.
Ministan ya kuma bayyana cewa FEC ta amince da aiwatar da gyaran gaggawa da aka yi wa babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu )International Conference Centre), wanda aka sabunta domin taron majalisar ECOWAS da aka gudanar a baya. Ya ce aikin ya kammala cikin lokaci kuma an buɗe shi bayan tabbatar da cewa ya kai matsayin ƙasa da ƙasa.
Haka zalika, Wike ya bayyana cewa FEC ta amince da sabunta ƙwangilar samar da gine gine a sabon yankin Maitama 2, wanda ya mamaye fili sama da hekta 786. Ya ce aikin ya tsaya tun shekaru biyar da suka wuce, amma yanzu an sake farfaɗo da shi domin bunƙasa sabon yankin birnin. “Wannan yana daga cikin manyan ayyukan babban birnin tarayya ake aiwatarwa, kuma gwamnati za ta tabbatar da an kammala shi cikin nasara,” in ji shi.














