• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

by Sani Anwar
7 hours ago
Nijeriya

‘Yan Nijeriya da dama da suka hada da jami’an diflomasiyya da lauyoyi da kungiyoyin yankuna, sun yi tir tare da Allah-wadai da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi, na mamaye kasar da sojoji, kan zargin kisan kiyashin da ake yi wa kiristoci.

Jami’an diflomasiyya sun bayyana cewa, ko kadan ba su amince da duk wani matakin soja da Amurka za ta dauka ba, amma kuma sun bukaci gwamnatin tarayya; ta kawo karshen rashin tsaron da ya addabi kasar.

  • Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
  • Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

Sun kuma yi kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya nada sabbin jakadu.

Mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, a cikin wani sako da ya fitar a shafinsa na D a ranar Lahadi, ya ce; a ranar Alhamis ne shugaban kasar ya shaida wa sabbin shugabannin ma’aikatan tsaro abin da ‘yan Nijeriya ke tsammani daga gare su.

Fadar shugaban kasar ta kuma bayyana cewa, Tinubu zai gana da shugaban kasar Amurka, nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, domin tattaunawa kan zargin.

LABARAI MASU NASABA

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Trump ya sake mayar da Nijeriya matsayin kasa mai matukar damuwa, sannan ya yi gargadin cewa; “idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bayar da izinin kashe kiristoci, nan take Amurka za ta dakatar da duk wani taimako da take bai wa Nijeriya, sannan kuma mai yiwuwa ta shiga kasar, domin kakkabe ‘yan ta’addan Islama da ke aikata wadannan munanan ayyuka na ta’addanci.”

Kazalika, ya kuma umarci Ma’aikatar Yakin Amurka, da ta shirya domin daukar mataki.

Pete Hegseth, Sakataren Yakin Amurka, a ranar Asabar ya ce; Ma’aikatar Yaki na shirin daukar mataki.

Barazanar Trump dai, ta biyo bayan zargin da wani dan majalisar dokokin Amurka, Ted Cruz, ya yi a shafinsa na D, a ranar 7 ga watan Oktoba na cewa; an kashe kimanin kiristoci 50,000, tun daga shekarar 2009 tare da lalata makarantu 2,000 da rusa Coci-coci 18,000, wanda musulmi masu dauke da makamai suka dauki nauyin aikatawa. Sai dai Cruz, bai ambaci tushen bayanan nasa ba.

A martanin da ya mayar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a ranar Asabar da ta gabata, ya yi watsi da zargin da Trump ya yi wa Nijeriya, yana mai dagewa kan cewa; kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayin dimokuradiyya mai tushe da tsarin mulkin kasar ya ba da ‘yancin yin addini.

A cewarsa, Nijeriya ta tsaya tsayin daka a matsayin dimokuradiyyar da kundin tsarin mulki ya ba da ‘yancin walwala.

Ya ce, tun daga shekarar 2023, gwamnatinsa ta ci gaba da kasancewa tare da shugabannin Kiristoci da na Musulmi baki-daya, sannan kuma tana ci gaba da magance matsalolin tsaro da suka shafi ‘yan kasa a fadin addinai da yankuna daban-daban.

“Yancin addini da juriya, sun kasance ginshikin tushenmu, kuma za su ci gaba da kasancewa a haka, Nijeriya na adawa da zalincin addini, sannan kuma ko kadan ba ta karfafe shi ba.

“Nijeriya kasa ce da kundin tsarin mulkinta ya bayar da tabbacin kare ‘yan kasa a kowane addini.

Gwamnatinmu, ta kudiri aniyar yin aiki tare da gwamnatin Amurka da sauran kasashen duniya, domin zurfafa fahimta da hadin gwiwa, kan kare al’ummomin dukkanin addinai,” in ji Tinubu.

Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, a wata sanarwa da kakakinta, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya fitar a ranar Asabar ya ce: “Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, ta lura da kalaman da shugaban kasar Amurka Donald J. Trump, ya yi a baya-bayan nan, game da kashe-kashen kiristoci da ake yi a Nijeriya tare da yin kira da a ayyana kasar a matsayin “Kasar da za a mayar da hankali a kai.”

“Yayin da Nijeriya ta yaba da damuwar duniya game da ‘yancin Dan’adam da ’yancin addini, wadannan ikirari, ba su nuna halin da ake ciki a kasar ba, ‘yan Nijeriya na dukkanin addinai, sun dade suna rayuwa tare, suna yin aiki tare, sannan kuma suna yin ibada tare a cikin lumana.

“A karkashin jagorancin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya ta jajirce wajen yaki da ta’addanci, karfafa hadin kan addinai da kare rayuka da ‘yancin al’ummarta.

“Nijeriya za ta ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Amurka, don zurfafa fahimtar juna game da yanayin yankin da kuma kokarin da ake yi na zaman lafiya da tsaro.”

 

Su Ma Musulmin Ana Kashe Su- Yankin Middle Belt

Shugaban Kungiyar ‘Middle Belt’ (MBF), Dakta Bitrus Pogu, ya bayyana cewa; ‘yan ta’addan kasar nan ne suke kashe musulmai kamar yadda suke kashe Kiristoci.

Ya ce, barazanar da Amurka ta yi, kira ne kawai na farkar da gwamnatin Nijeriyar, domin murkushe ‘yan ta’adda.

Ya kara da cewa; “Amurka ba ta fitar da wata barazanar daukar matakin soji ba, illa kawai ta sanya Nijeriya a matsayin kasa wadda ya kamata a sanya wa ido.

“Hakan yana nufin sanya takunkumi, shiga tsakani don tabbatar da cewa; an tilasta wa gwamnati yin abin da ya dace, sannan kuma; idan har za a dauki wani mataki na soja, wato na fatattakar ‘yan tada kayar baya, ba za a zama kasa daya ba, kana kuma; hakan zai faru ne kawai idan kasarmu ta ki yin abin da ya kamata ta yi.

“Haka zalika, a koda-yaushe na sha fadin cewa; sojojinmu na kokari kwarai da gaske, amma akwai masu zagon kasa a cikin jami’an tsaron, kuma daga lokaci zuwa lokaci, an yi ta samun hakan kamar a zamanin marigayi Buhari.

“Ana kashe mutane daruruwa babu wanda ya damu, sannan babu wanda aka kama a tsakanin mutanen da suke kai wannan hari, wadannan mutane za su zo su kai hari, amma har sai an bai wa sojoji umarni kafin su yi wani abu a kai ana ji ana kallo.

“Don haka, batu na gaskiya akwai matsala, sannan abin takaici kuma shi ne, duk wadannan kungiyoyi masu tayar da kayar baya a Arewa, suna kashe Kiristoci ne da kuma Musulmai, kana kuma suna kiran kungiyarsu da ta jihadi, wadanda a zahiri ba Musulmai ba ne.

 

Kungiyar ACF Ta Musanta Zargin Kisan Kiristoci Kadai

Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF), a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadin da ta gabata, ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ta yi gargadi game da mamayar da kasashen waje ke yi wa wata kasa mai cin gashin kanta ta Amurka.

ACF ta kuma yi nuni da cewa, ‘yan ta’adda a kasar nan, na kashe ‘yan Nijeriya daga kowane irin addini.

“Tare da dimbin bayanan sirrin da aka tura ko’ina, ya kamata a ce, Amurka ta fi kowa sanin halin da ake ciki na kisan da ake yi.

“Kamar sauran ‘yan Nijeriya masu kishin kasa, mambobin kungiyar tuntuba ta Arewa, sun samu labari mai cike da takaici game da ayyana Nijeriya a matsayin kasar da Amurka ta sanya wa ido,” in ji shi.

“Tuni dai ‘yan Nijeriya na kowane bangare na fama da hare-haren da wasu bata gari da suka hada da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga, ‘yan tada kayar baya da masu tsattsauran ra’ayin addini a yankin Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma, Kudu maso Gabas da sauran sassan kasar nan.

Ya kara da cewa “Shekaru da dama, kungiyar ACF na sane da cewa; gwamnatocin Nijeriya da suka biyo baya, sun roki Amurka da ta taimaka musu ba tare da wata fa’ida ba.”

Ya ce, duk wani tallafi daga kasashen waje ya kamata ya mayar da hankali wajen taimakawa sojojin Nijeriya, maimakon kai hari kan wata kungiyar addini.

Haka zalika, ACF ta gargadi ‘yan Nijeriya da su tuna da darussan tarihi, inda ta ambaci tsoma bakin da aka yi a Bietnam, Afghanistan, Syria, Irak da kuma kusa da gida, akwai Libya da Sudan, da kasashen Sahelian, har sai sun sake tunani, don lissafta wasu kadan.

Taron ya yi maraba da martanin da gwamnatin tarayya ta bayar, inda ta bayyana cewa; ya cancanci goyon bayan duk wanda abin ya shafa.

ACF ta kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su yi tunani mai zurfi game da lamarin tare da marawa gwamnati baya, yayin da take mayar da martani kan lamarin, sannan ta yi kira ga hadin kan yankin daga “Afirka da sauran kasashe.”

A cewar sanarwar: “Bisa la’akari da babban tasiri ga aikin Nijeriya, ACF za ta ci gaba da sa ido, tantancewa da kuma mayar da martani ga ci gaban al’amarin.”

Har ila yau, shugabannin addinai daban-daban a fadin wadannan kasa tare kuma da wasu jiga-jigai a fannin siyasa da sarakuna, sun yi watsi da wannan zargi na Kasar Amurka tare da barazanar da suka yi na kawo wa Nijeriya hari.

Baya ga watsi da wannan barazana da Trump ya yi, Rabaran John Joseph Hayab, ya yi kira ga Kiristoci da Musulmi daga Arewacin Nijeriya da su gudanar da tarukan hadin kai da zaman lafiya.

Rabaran Hayab, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), na Jihohin Arewa 19 da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT), ya ci gaba da ba da shawarar a rika tattaunawa tsakanin addinai, domin magance matsalolin da yankin ke fuskanta, kamar rashin tsaro da kuma rashin yarda da juna.

Haka nan, malaman addinin musulinci, kamar irin su Sheikh Ahamad Gumi, Sheikh Ibrahim Makari, Sarkin musulmi da sauran ‘yan siyasa kamar irin su Sanata Rabi’u Kwankwaso, Sanata Shehu Sani da Manjo Hamza Almustapha, sun yi kakkausan martani a kan wannan barazana da Kasar Amurka ta yi.

A ranar Talatar da ta gabata ne, Kasar Sin; ita ma ta shiga jerin cikin wadanda suka yi watsi da barazanar da Amurkan ta yi, na daukar matakin soji kan Nijeriya, tana mai cewa; tana matukar adawa da duk wani katsalanda daga waje a cikin harkokin cikin gidan kasar.

Matsayin gwamnatin kasar ta Sin, ya zo ne a ranar da gwamnatin tarayya ta ce; masu tsattsauran ra’ayin addini ne ke bayan wannan labari na zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci, tare da cewa; babban burinsu shi ne, raba kan al’umma.

Ita ma a nata bangaren, Majalisar Dinkin Duniya; ta yi kira ga kasashe da su guji amfani da karfi, dangane da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Nijeriya, kan zargin kisan kiyashi da aka ce ana yi wa Kiristoci.

Har ila yau, a cikin jawabai daban-daban, Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), sun yi gargadi kan ayyukan da za su iya yi wa Nijeriya zagon kasa, inda suka dage cewa; ta’addanci a yankin ya shafi dukkanin mabiya addinan guda biyu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah
Manyan Labarai

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 
Manyan Labarai

Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

November 7, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Next Post

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

LABARAI MASU NASABA

GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

November 7, 2025
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

November 7, 2025
Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.