Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne, sun kashe wani babban limami da wasu masu ibada uku yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban a lokacin da ‘yan ta’addar suka kai hari a kauyen Ngulde da ke karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno.
LEADERSHIP ta rawaito cewa ‘yan ta’addar wadanda yawansu ya kai 20, sun kaddamar da harin ne a ranar Juma’a, inda suka bude wuta kan masallatan bayan sun idar da sallar Fajir a masallacin.
- ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Masunta A Tafkin Chadi
- An Kashe ‘Yan Boko Haram 49 A Sansaninsu 3 Yayin Luguden Wuta Ta Sama
Rahotanni sun ce ‘yan ta’addar sun yi awon gaba da dabbobi da kayan abinci tare da kona motoci biyu a yankin Ngulde da ke wani yanki na dajin Sambisa a jihar.
Da yake tsokaci kan harin, Kansila mai wakiltar Ngulde Ward a karamar hukumar Askira-Uba, Hon. Bilyaminu Umar, ya mika sakon ta’aziyya da jajantawa ga daukacin al’ummar mazabarsa kan harin da mayakan Boko Haram suka kai musu, wanda ya afku a ranar 2 ga Satumba, 2022.
Ya ce, “Mazabar Ngulde na daya daga cikin mazabun da al’ummar karamar hukumar Askira-Uba suka ba ni izinin wakiltarsu a zaben kananan hukumomin da ya gabata. Tun daga wannan lokacin, ina jin daɗin haɗin kai da goyon bayansu. Don haka, na ji matukar kaduwa da jin bakin cikin wannan sabon hari, lokacin da yawancin mutanena suka shagaltu da yin amfani da lokacin noman bana.
“Harin wanda ya faru da sanyin safiyar Juma’a, 2 ga watan Satumba, 2022, bayan sallar Fajir, ya yi sanadin mutuwar mutane hudu (4) tare da jikkata wasu da dama, yayin da kuma wasu ‘yan bindiga suka lalata dukiyoyi da wuraren kasuwanci na miliyoyin naira da tayar da kayar baya.
“Tuni na sanar da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Hon. Engr Abdullahi Askira, akan kai harin na rashin tausayi. Ya yi alkawarin isar da shi ga Gwamnan Jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum, domin daukar matakin da ya dace.”
Da aka tuntubi mataimakin kakakin majalisar jihar Borno, wanda kuma ke wakiltar mazabar Askira-Uba, Abdullahi Askira, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “Eh, na samu kiran waya jiya cewa wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki garin Ngulde inda suka kashe mutane uku nan take, yayin da wani mutum daya kuma ya rasu a hanyar zuwa asibitin Garkida inda aka garzaya da wadanda suka jikkata domin yi musu magani.
“Masu tayar da kayar bayan sun kai kimanin 20, sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 6:30 na safe, inda suka nemi a nuna musu wuri ko gidan shugaban mafarauta/’yan banga.
“Ba tare da bata lokaci ba, kai tsaye suka je wajen wasu masallata da suka kammala Sallar Fajir a Masallaci suka bude wuta, lamarin da ya kai ga kashe mutane uku nan take, ciki har da babban limamin sashin Gima.”