A ranar Talata, an samu tashin hankali a shalkwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja bayan ‘yan daba daga ɓangarori biyu da ke taƙaddama da juna sun yi artabu a ofishin jam’iyyar.
Rigimar ta fara ne da sassafe lokacin da magoya bayan dakataccen sakataren jam’iyyar, Sanata Samuel Anyanwu, suka iso wajen da misalin ƙarfe 8 na safe.
- Zaɓen 2027: Malami Zai Fito Takarar Gwamna A Kebbi
- ’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi
Sun ce sun isa ofishin ne domin karɓar ragamar jam’iyyar bayan gudanar da taron jam’iyyar a makon da ya gabata.
Amma magoya bayan shugaban jam’iyyar na riƙon kwarya, Ambasada Umar Damagum, suka taru domin hana su shiga.
Lamarin ya yi ƙamari, inda ‘yan daba daga ɓangarorin biyu suka afka wa juna da faɗa.
’Yansanda da ke wajen sun yi ƙoƙarin kwantar da tarzomar, duk da cewa manyan jam’iyyar kamar Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, suna wajen.
Daga ƙarshe, ’yansanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa su.
Wannan ya sa ’yan jarida, ma’aikata da mambobin jam’iyyar suka nemi mafaka, yayin da wasu mutane suka ji rauni.
Rikicin ya yi sanadin lalata wasu kadarorin hedikwatar jam’iyyar.
Saboda wannan tashin hankali, sabon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya sanar da ɗage taron farko na kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) da aka shirya yi a ranar Talatar.
Da yake magana da ’yan jarida, Turaki ya ce an ɗage taron zuwa ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamba.
Ya zargi “maƙiyan ci gaba da maƙiyan dimokuraɗiyya” da haddasa rikicin.
Turaki, ya gode wa Kwamishinan ’Yansandan Abuja, saboda samar da tsaro.
Ya kuma yaba wa gwamnoni, ’yan majalisa, tsofaffin ministoci, shugabannin jam’iyya da sauran manyan jam’iyyar saboda goyon bayansu.
Ya ce PDP jam’iyya ce mai son zaman lafiya, kuma dole ta ci gaba da kasancewa a haka domin samun damar kowawa mulki.
Rikicin shugabanci ya ƙara tsananta bayan da jam’iyyar ta kori Samuel Anyanwu, Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wasu da ake zargi da cin amanar jam’iyyar.
Magoya bayansu su ma sun shirya yin nasu taron a hedikwatar jam’iyyar a ranar Talata, lamarin da ya ƙara dagula al’amura.














