Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya dakatar da bikin komawarsa jam’iyyar APC saboda sace wasu ɗalibai 25 a makarantar ’yan mata da ke Maga, Jihar Kebbi.
An shirya taron tarbarsa zuwa APC ne a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamba 2025, a filin wasa na Jolly Nyame da ke Jalingo, kuma an gayyaci manyan baƙi ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.
- Binciken CGTN: Batun “Barazanar Dorewar Kasa” Ba Komai Ba Ne Illa Nuna Babakeren Japan
- PDP Ta Ɗage Taronta Bayan Arangamar ‘Yansanda Da ‘Yan Daba A Abuja
Gwamna Kefas ya ce sace ɗaliban babban abun takaici ne da ke nuna taɓarɓarewar matsalar tsaro a ƙasar nan.
Ya ce kare rayuwar yara ya fi kowanne abu muhimmanci sama da harkokin siyasa.
Ya jajanta wa iyayen ɗaliban da aka sace, sannan ya buƙaci jami’an tsaro su ƙara himma wajen ceto su.
Za a sanar da sabuwar ranar da taron zai gudana daga baya.
A wani labarin kuma, shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Taraba, Alhaji Abubakar Bawa, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa APC.
Ya ce rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi ne ya sa ya yanke wannan shawara.
Bawa ya ƙara da cewa shi da magoya bayansa sun koma APC ne tare da goyon bayan Gwamna Kefas.














