Jakadan Sin a Nijeriya Cui Jianchun, ya gana da ministan yada labarai da raya al’adu na Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed, inda ya gabatar masa da dabarun samun ci gaba da nasara, a dangantaka da musaya tsakanin Sin da Nijeriya a fannoni daban daban a nan gaba.
Ya kuma yi bayani kan muhimmancin da yayata al’adun kasar Sin zai yi wajen kyautata alaka tsakanin kasashen biyu.
Ya kuma jaddada cewa, nasarar taron karamin kwamitin al’adu da yawon bude ido dake karkashin kwamitin kula da huldar kasashen biyu a farkon wannan shekara, ya samar da muhimmin dandali na karawa musaya tsakanin al’ummomin kasashen biyu kuzari.
A nasa bangare, Lai Mohammed ya yabawa dabarar samun ci gaba da nasara da jakadan na Sin ya gabatar, da kuma tunanin kyautata alaka ta hanyar al’adu, yana mai cewa, zai jagoranci kasashen biyu wajen inganta dangantakarsu a aikace, a fannoni daban daban. (Fa’iza Mustapha)