Kwamishinan tsara gine-gine da tsara birane na jihar Legas, Dakta Idris Salako ya yi murabus daga Majalisar zartaswar gwamna Babajide Sanwo-Olu, sakamakon ruftawar wani Gini A Oniru da ke Lekki a jihar Legas.
LEADERSHIP ta labarto cewa mutum biyar ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan da wani gini mai hawa bakwai da ake kan aikinsa ya rufta da safiyar ranar Lahadi.
Kan bakan, sakamakon ruftawar ginin, gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya amince da murabus din kwamishinan a ranar Litinin.
A wata sanarwar manema labarai da kwamishinan yada labarai na jihar, Gbenga Omotoso, ya ce murabis din kwamishinan na daga cikin kokarin da ake kan yi na sake fasalin ma’aikatar da rassan da ke karkashinta.
“Gwamna Sanwo-Olu ya gode wa kwamishinan bisa aiki a karkashinsa da kokarin hidimta wa jihar ya masa fatan alkairi a rayuwarsa na gaba.
“Gwamnan ya gargadi dukkanin masu ruwa da tsaki a lamarin da suke bin doka da ka’ida ko su fuskanci fushin gwamnatinsa,” ya ce kowaye ba za a sarara masa ba.