Yau Jumma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta jagoranci taron manema labarai na yau da kullun, inda game da matakin kasar Japan na tattaunawa tare da gyara “Ka’idoji uku na hana yada makaman nukiliya”, Mao Ning ta bayyana cewa, komawar Japan hanyar nuna karfin soja, na nufin karya alkawarinta na samun ci gaba ta hanyar zaman lafiya, da kuma lalata tsarin kasa da kasa bayan yaki, kuma al’ummun Sin ba za su amince da hakan ba, kana al’ummun duniya ma ba za su yarda da hakan ba, daga karshe kuma Japan din za ta gamu da rashin nasara.
Mao, ta kuma bayyana cewa, idan Japan tana son habaka dangantaka ta moriyar juna bisa tsare-tsare tsakaninta da Sin, ya kamata nan take ta janye kalamanta na kuskure game da Taiwan. Har ila yau, ya kamata al’ummun duniya su sanya ido don ganin ko Japan za ta dage wajen bin hanyar ci gaba cikin lumana ko a’a. (Safiyah Ma)














