Tsakanin jiya Asabar da yau Lahadi firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci zama na biyu da na uku na taron kolin G20 karo na 20 a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu, inda ya gabatar da jawabi kan batutuwan da suka shafi gina duniya mai dorewa, da samar wa daukacin bil’adama makoma mai adalci daidai-wa-daida.
Firaministan ya bayyana cewa, a halin yanzu duniya na fuskantar kalubalolin sauyin yanayi, da makamashi, da abinci da sauransu. Don haka ya dace kasashen G20 su taimaka wajen habaka hadin-gwiwar sassan kasa da kasa, da shawo kan kalubaloli cikin hadin-gwiwa, da samar da ci gaba tare, gami da karfafa hadin-gwiwa a fannonin da suka shafi kiyaye muhalli, da raya makamashi mai tsafta, da samar da wadataccen abinci, da bunkasa kimiyya da fasahar aikin gona da sauransu.
Li ya kuma ce, ana gaggauta raya sabon zagayen juyin-juya-halin kimiyya da fasaha, gami da yin garambawul ga sana’o’in duniya. Ya kamata kasashen G20, su tsaya ga bude wa juna kofofi da neman cimma alfanu tare, da more damammaki, da zummar kara samar da alherai ga al’ummomin kasa da kasa. Har wa yau, ya jaddada muhimmancin taimaka wa kasashe masu tasowa, ciki har da na Afirka, a fannin inganta kwarewar neman ci gaba, da samar da karin guraban ayyukan yi, da bunkasa harkokin mata da matasa.
An zartar da sanarwar shugabanni kan taron kolin G20 na Afirka ta Kudu.
A yayin taron kolin ma, firaministan Li ya yi shawarwari tare da shugabannin kasashen Faransa, da Koriya ta Kudu da Angola, da firaministan kasar Sifaniya, da kuma babbar darektar kungiyar kasuwanci ta duniya wato WTO. (Murtala Zhang)














