Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda ya kai Naira biliyan 878.15, ga majalisar dokokin jihar don amincewa da shi.
Ya yi bayanin cewa an ware biliyan 567.47 (kaso 65%) domin manyan ayyuka, sannan biliyan 312.69 (kaso 35%) domin ayyukan yau da kullum.
- Sarkin Musulmi Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
- Sin Ta Ciri Tuta A Jagorancin Ayyukan Dakile Sauyin Yanayi
Gwamnan ya ce za a raba ayyuka cikin adalci a dukkanin yankunan jihar.
Ya roƙi majalisar ta yi gaggawar duba kasafin don a fara aiwatar da shi a kan lokaci.
Ya ƙara da cewa an fi mayar da hankali kan ilimi, lafiya, noma, inganta karkara da birane, ruwa da samar da ayyukan yi.
Ya ce ana son ci gaba da ayyukan da aka fara a 2025 tare da inganta rayuwar jama’a.
Kakakin majalisar, Abubakar Y. Sulaiman, ya gode wa gwamna, ya kuma yi alƙawarin cewa majalisar za ta yi aiki a kan lokaci wajen nazari da amincewa da kasafin domin ci gaban jihar.














