Bayan shafe watanni ana gudanar da bincike, hukumomin kasar Sin sun bankado kutsen da aka yi wa jami’ar kimiyya da fasaha ta arewa maso yammacin kasar wato NPU.
Rahotannin binciken da aka fita a jiya, sun bayyana yadda ofishin tattara bayanan sirri ta intanet na TAO na ma’aikatar tsaron Amurka NSA, ya yi amfani da hanyoyi 41 wajen yi wa jami’ar NPU kutse tare da satar bayanan wasu muhimman fasahohi.
Ta’addanci ba ya nufin daukar makami da kaddamar da hare-hare kadai, kutsen intanet ma wani nau’i ne na ta’addanci, domin irin illolin da zai iya haifarwa da ba za su iya misaltuwa ba.
Kasashe da hukumomi da al’ummomi har ma da daidaikun mutanen duniya sun fi mayar da hankali ne kan gudanar da harkokinsu ta intanet har ma da adana muhimman bayanan sirri, kasancewarta fasaha ta zamani kuma mai saukin amfani.
Sai dai kuma, wasu na daukarta a matsayin makami na liken asiri da tsaiko ga ci gaban kasashe.
Kutsen intanet da Amurka ta yi, ya bayyana ainihin abun da take fakewa da shi da sunan tsaron kasa ko intanet.
A ko da yaushe, ta kan fake da tsaron kasa ko intanet, wajen zartar da dokoki marasa ma’ana ko zargin wasu da yi mata kutse, ashe dai, abun da take yi ne take gudun a yi mata, kamar dai yadda ake cewa, “wanzam bai son jarfa”.
Ko a baya-bayan nan, ta hana sayarwa kamfanonin kasar Sin kananan na’urorin laturoni da sunan kiyaye tsaron kasa, wanda wani salo ne da ta bullo da shi domin habaka kasuwar nata kamfanoni.
Hakika wannan yunkuri zai kara tayar da hankalin al’ummomin duniya, domin ya nuna cewa, babu wanda zai iya tsira daga kutsen.
Sam bai dace a ce ana samun irin haka daga kasa kamar Amurka da a kullum take nanata batun tsaron kasa ko kare hakki ko tsaron intanet ba.
Domin bayan aikin ta’addanci, kutse intanet, wani nau’i ne na keta hakkin jama’a da ma tsaron sirrikansu.(Fa’iza Mustapha)