Jakadan Bangladesh a Nijeriya, Mista Miah Mainul Kabir, ya yi kira da a kafa reshen Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) a ƙasar Bangladesh.
Mista Mainul Kabir ya bayyana wannan buƙata ne a lokacin da ya ziyarci MAAUN Kano a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa buɗe reshen MAAUN a Bangladesh zai ƙara fito da jami’ar a idon duniya wajen haɓaka ilimi da basirar ƙere-ƙere a matakin ƙasa da ƙasa.
- Gwamnatin Kano Ta Fara Ɗaukar Matakan Daƙile Dawowar Masu Achaba
- Yaushe Ne Ƙarshen Rikicin Yajin Aiki Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Tarayya A Nijeriya? (2)
Jakadan ya yaba wa MAAUN bisa yadda shahararta yake ƙaruwa wajen ingancin karatu da bincike kan ƙirkire-ƙirkire, yana mai cewa jajircewar jami’ar wajen ƙirƙira ta zama abin koyi ga sabbin jami’o’i a faɗin duniya.
Jakadan ya kasance a jami’ar ne domin gabatar da lacca mai taken: “Amfani da Ƙwarewar Matasa wajen Tattalin Arziki da Cigaban Zamantakewa.”
Laccar wadda Ofishin Jakadancin Bangladesh da ke Abuja tare da haɗin gwiwar MAAUN suka shirya, ta yi nufin ƙarfafa matasa domin gina kyakkyawar makoma ga kansu da ƙasa baki ɗaya.
Tun kafin fara laccar, hukumar gudanarwar jami’ar da jakadan Bangladesh da tawagarsa sun yi dogon zama kan fannoni daban-daban na yiwuwar haɗin gwiwa tsakanin jami’ar da ƙasar Bangladesh.
Ya jaddada ƙoƙarin da ofishin jakadancin ke yi na tuntuɓar gwamnatoci, cibiyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin samar da haɗin gwiwar da za ta haifar da ci gaba mai ma’ana.
Daga bisani, an zagaya da Jakadan da tawagarsa wasu muhimman sassa na jami’ar, ciki har da MAAUN Innovation Hub da ke cikin School of Computing, inda ya duba kayan aiki da ake amfani da su a wurin.
A jawabinsa na maraba, Shugaban MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr, ya ce wannan lacca daga jakadan Bangladesh shaida ce ta jajircewar MAAUN wajen gina haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa da kuma ƙarfafa matasa.
Ya jaddada buƙatar samar wa matasa ƙwarewa, ilimi da damar da ake buƙata domin su taka rawar gani wajen kawo cigaba mai ma’ana.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Jami’ar (ɓangaren gudanarwa), Dr. Habib Awaisu Abubakar, ya yaba wa Ofishin Jakadancin Bangladesh da kuma MAAUN bisa yunƙurin faɗaɗa haɗin gwiwa domin ƙarfafa fannin ilimi da ci gaba.
A yayin gabatar da takardarsa, Jakadan ya bayyana muhimmancin rawar da matasa ke takawa wajen sauya tattalin arziƙi da zamantakewa, yana mai cewa Bangladesh da Nijeriya dukkansu suna da yawan matasa masu kuzari waɗanda suke da babbar damar amfani.
Ya kawo misalan ƙirkire-ƙirkiren matasa, haɗin gwiwar duniya da cigaban zamantakewa, yana mai bayyana cewa matasa a sassa daban-daban na duniya suna taka rawar gani wajen kawo canji.
Ya kuma ce ɗaliban MAAUN suna cikin sahun gaba wajen wannan tafiya ta duniya, yana yabawa jami’ar saboda ingantaccen yanayin koyarwa, hangen nesa na shugabanci da jajircewar da take da shi wajen ci gaban ɗalibai.
A ƙarshe, shugaban ‘School of Postgraduate’ na jami’ar, Farfesa Ibrahim Maigari, ya yaba wa jakadan Bangladesh saboda zaɓar MAAUN a matsayin jami’ar da za ta karɓi irin wannan muhimmin taro.














