Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov, sun yi kira da a kare nasarar da aka samu daga yakin duniya na II, yayin tattaunawar da suka yi jiya Talata a Moscow.
Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce bisa jagorancin shugaba Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimr Putin, dangantakar kasashen biyu ta kai wani babban matsayi a bangarori da dama, kuma tana samun ingantaccen ci gaba.
Ya kara da cewa, ya kamata Sin da Rasha su ci gaba da hada hannu da dagewa wajen yaki da ayyukan takala na Japanawa masu ra’ayin rikau dake barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin a wani yunkuri na sake jibge sojoji a yankin.
A nasa bangare, Sergei Lavrov ya ce shugabannin biyu sun ziyarci juna a bana, lamarin da ya kara karfafa dangantakarsu mai muhimmanci bisa manyan tsare-tsare. Ya kuma nanata goyon bayan Rasha ga manufar Sin daya tilo da matsayar Sin din kan batun Taiwan. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














