A kwanakin baya, an nuna wasu fina-finai guda biyu na kasar Sin a bikin fina-finai na kasa da kasa na Zuma karo na 15 a birnin Abuja dake kasar Najeriya. Daya daga ciki shi ne na “Rooting” wanda ya yi bayani kan yadda ake kokarin kawar da talauci a kasar Sin, dayan kuma shi ne na “Shen Zhou 13” wanda aka yi bayani kan nazarin sararin samaniya a cikin kumbon Shenzhou-13.
Direktan cibiyar al’adun kasar Sin ta Najeriya Yang Jianxing, da shugaban hukumar shirya fina-finai ta Najeriya Ali Nuhu, da jami’an hukumomin al’adu da yawon shakatawa da sabbin fannonin tattalin arziki da ba da ilmi da sauransu na gwamnatin Najeriya suka halarci bikin.
Yang Jianxing yana fatan fina-finan biyu da aka nuna za su sa kaimi ga abokan Najeriya da su kara fahimtar kasar Sin a dukkan fannoni. Kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa tare da Najeriya a fannin al’adu, da sa kaimi ga yin mu’amala da juna a tsakanin masu tsara fina-finai na kasashen biyu, da kara fahimtar juna da sada zumunta a tsakanin jama’ar kasashen biyu.
A nasa bangare, Ali Nuhu yana fatan za a zurfafa hadin gwiwa da mu’amala da juna a tsakanin bangarorin masu tsara fina-finai na kasashen biyu ta hanyar bikin.
Bayan kallon fim din, wani dalibin jami’ar Najeriya mai suna Rosper Dania ya bayyana cewa, ya ji dadin ganin yanayin sararin samaniya ta hanyar kallon fim, zai kara yin kokarin karatu don sa kaimi ga sada zumunta a tsakanin Najeriya da Sin, da kuma samar da gudummawa ga kasarsa ta Najeriya wajen raya sha’anin nazarin sararin samaniya. (Zainab Zhang)














